Laftanal Kanal Girbo ya na ganin zai iya kauda Boko Haram a watanni

Laftanal Kanal Girbo ya na ganin zai iya kauda Boko Haram a watanni

Laftana Kanal Adamu Girbo Muhammad mai ritaya, ya yi wata doguwar hira da jaridar Daily Trust inda ya bada labarin yadda ya shiga gidan soja, da irin hidimar da ya yi wa kasa da wasu batutuwan.

Adamu Girbo Muhammad asalinsa Direba ne kafin ya tafi gidan soji, ya bada labarin yadda Marigayi Abubakar Gumi ya sa ya shiga aikin soja a matsayin kurtu, har ta kai ya zama babban jami’in kasar.

Wannan tsohon Soja wanda ya bautawa Najeriya na tsawon shekaru 35 ya samu kai wa matsayin Laftanal Kanal kafin ya ajiye khaki, ya na kuma cikin wadanda su ka je a ka yi yakin basasa da su na Biyafara.

Da a ka yi wa tsohon sojan tambaya a game da yakin Boko Haram, ya bayyana cewa idan a na da bukatar shawarar tsofaffin Jarumai irinsu, za a iya shawo kan rikicin ‘yan ta’addan cikin wani karamin lokaci.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari sun kashe jama'a a Katsina

A cewar Laftana Kanal Adamu Girbo mai ritaya, shawarwarin da zai bada za su taimakawa jami’an tsaro wajen kawo karshen rigimar ‘yan Boko Haram a Najeriya a cikin watanni uku da yardar Ubangiji.

A lokacin ya na gidan soja, Adamu Girbo ya yi yakin basasa, sannan kuma ya na cikin Dakarun Najeriya da a ka rika aikawa kasashen ketare irin su Labanan da Liberiya domin kwantar da tarzoma.

Bayan nan kuma tsohon sojan ya bayyana cewa babu irin gumurzun da bai gani ba a lokacin ya na filin daga, har ya taba daukar makamai daga Owerri har Enugu, kuma ya yi karo iri-iri da Abokan gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel