Mai Sha'awar Neman Kujerar Barau Ya Fadi dalilin Ganawarsa da Shettima, Ganduje
- Tsohon minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayyana dalilin ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
- Gwarzo ya ce sun yi ganawar da Abdullahi Umar Ganduje wacce ta mayar da hankali kan siyasar Kano ta Arewa da makomar APC
- Ya ce ya shiga takarar kujerar sanatan Kano ta Arewa domin samar da wakilci mai kyau duk da rikicin jam’iyya da ake dangantawa da Barau Jibrin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon minista a Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya tabbatar da neman takarar kujerar sanatan Kano ta Arewa.
Gwarzo ya bayyana dalilin ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a birnin Abuja.

Source: Facebook
Gwarzo ya ce sun tattauna kan siyasa da kuma harkokin Kano ta Arewa domin kawo sauyi a yankin kamar yadda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP
Tsohon minista ya gana da Ganduje, Shettima
Rahotanni sun nuna cewa Gwarzo ya halarci ganawar tare da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Abubakar Kabir Bichi.
Ya ce Shettima ya yi musu fatan alheri a harkokinsu na siyasa domin samun jagoranci na gari.
Ganawar ta zo ne bayan Gwarzo ya bayyana aniyarsa ta kalubalantar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, domin kujerar Kano ta Arewa.
Tsohon ministan gidaje na kasa ya ce yana son samar da sahihin wakilci ga yankin wanda ya dade a cikin wani irin yanayi tun bayan dawowar dimukradiyya.
Shigowar Gwarzo cikin takarar ya kara dagula siyasar cikin APC, yayin da ake zargin akwai yunkurin hana shi tsayawa takara kafin zaben fidda gwani na ranar 18 ga Mayu.
Gwarzo ya kuma zargi Barau da hannu wajen hana shi nasara a wata takarar baya yayin da yanzu ya shirya fafatawa da shi domin nema wa yankin jagoranci na gari.

Source: Facebook
Hasashen ganawar Gwarzo da Shettima, Ganduje
Ana ganin ganawar da aka yi da Shettima wata hanya ce ta neman goyon bayan manyan APC domin karfafa matsayin Gwarzo kafin zaben fitar da gwani.
Masu sharhi na ganin goyon bayan Ganduje da Bichi na iya kara masa karfi a siyasar Kano ta Arewa duk da cewa Barau Jibrin ne ke rike kujerar a yanzu.
A baya, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta masu neman takarar sanatan Kano ta Tsakiya, inda mutum bakwai suka janye suka mara wa tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau, baya.
Sai dai har yanzu ba a yi irin wannan sulhu ba a Kano ta Arewa inda Abdullahi Gwarzo ke neman fafatawa da Barau Jibrin.
Abdullahi Gwarzo ya karyata barin APC
A baya, an ji cewa tsohon karamin Ministan raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya yi martani ga bayanan da ke cewa zai rabu da APC.

Kara karanta wannan
Rikicin Yobe: mutum 6 da aka hana takarar gwamna a APC sun gana da Kashim Shettima
Gwarzo ya yi annan bayani ne a yayin da jiga-jigan 'yan adawa da ke suke sauya sheka zuwa ADC da ke hamayya da mulkin Bola Tinubu.
Tun bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa ADC a makon da ya gabata siyasar Kano ta canja alkibla.
Asali: Legit.ng
