Abinda yasa na bude gidan radiyon makiyaya - Usman Shehu

Abinda yasa na bude gidan radiyon makiyaya - Usman Shehu

Usman Shehu, tsohon dan jarida ne da ya taba aiki da sashen Hausa na radiyon Amurka (VON) da gidan radiyon jihar Bauchi (BRC), yanzu haka kuma shine babban editan sashen Hausa na gidan radiyon Duetsche Welle (DW) da ke kasar Jamus.

Shine dan jaridar da ya kafa gidan radiyon 'Koode Radio International (KRI) da ke yada shirye-shiryenta cikin harshen Fulfulde.

Da ya ke bayyana dalilin kafa gidan radiyon KRI yayin wata hira ta musamman da jaridar 'weekly trust' ta yi da shi, Shehu, ya ce makasudin kafa gidan radiyon shine domin ilimantar wa, fadakar wa da nishadantar da dukkan Fulani.

Ya kara da cewa gidan radiyon KRI zai taka muhimmiyar rawa wajen magance yawaitar samun rigingimu a tsakanin manoma da makiyaya tare da samar da hanyoyin da kasa za ta iya inganta rayuwar Fulani makiyaya domin bunkasa tattalin arzikin ta.

A cewar Shehu, gidan radiyon KRI zai kawo raguwar amfani da Fulani makiyaya da wasu kungiyoyin ta'addanci ke yi ta hanyar fadakar da su, da yarensu, illolin da ke cikin yi wa irin wadannan kungiyoyi aiki. Kazalika, ya kara da cewa gidan radiyon zai wayar da kan Fulani makiyaya domin su zamanantar da harkar kiwo da kuma irin ribar da ke cikin harkar.

"Ta hanyar sadarwa ne kawai za a iya isar da sako. Za mu iya cimma manufar mu ta wayar da kan makiyaya ta hanyar kirkirar shirye-shirye da zasu ilimantar da wayar da su a cikin harshensu.

"Sashen Hausa na radiyon DW da nake yi wa aiki na yada shirye-shirye cikin harsunan duniya 30 amma babu yaren Fulfulde, haka lamarin ya ke a duk ragowar gidajen radiyo na duniya irinsu BBC da VOA.

"Sanin cewa duk inda Bafulatani ya ke ya na da sha'awar sauraren radiyo, shi yasa na yi tunanin kafa gidan radiyo da zai ke yada shirye-shirye cikin harshen Fulfulde domin isar da sako cikin sauki ga makiyaya a duk inda suke cikin fadin Najeriya," a cewar Usman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel