Kwankwaso Ya Haska Dalilin Arewa na Aiki da Peter Obi don Zaben 2027

Kwankwaso Ya Haska Dalilin Arewa na Aiki da Peter Obi don Zaben 2027

  • Madugun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zabi ya yi tafiya tare da Peter Obi domin fuskantar babban zaben 2027
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba haka nan kawai manyan siyasar Arewa auka zabi su yi aiki tare da Peter Obi ba
  • Tsohon gwamnan na Kano ya tuna baya kan yadda ya rika yin aiki tare da mutanen da ke a samansa da kuma kasansa a gwamnati

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya yi magana kan yin aiki tare da Peter Obi.

Kwankwaso ya bayyana cewa shugabannin siyasar Arewa sun gudanar da bincike na tsanaki kan abokan tafiyar da za su iya marawa baya kafin su amince da Peter Obi, a matsayin mafi cancanta don fuskantar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

2027: Yadda 'yar Kwankwaso ta shawo kan shi game da hada kai da Obi

Kwankwaso ya yi magana kan Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wajen taron NDC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tashar Arise TV ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayar da cikakken bayani kan yadda aka ƙulla ƙawancen siyasa tsakanin Arewa da Kudu maso Gabas a cikin jam’iyyar NDC.

Meyasa za a yi aiki da Peter Obi?

Ya yi watsi da damuwar da ake nunawa game da wani boyayyen rikicin neman iko tsakanin sansaninsa da na Obi.

“Na duba ko’ina tare da sauran shugabanninmu na Arewa domin mu ce, shikenan, wane ne muke tunanin zai iya? Wane ne zai zo mu yi aiki tare cikin gaskiya domin mu ciyar da ƙasar nan gaba?"
"A cikin wannan binciken, mun fahimci cewa Peter Obi ne yake kan gaba. Shi ya sa dukkanmu muka amince mu yi aiki tare."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Shin akwai adawa tsakanin Obi da Kwankwaso?

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hakura, ya shirya goyon bayan Peter Obi ko wani 'dan takara a zaben 2027

Yayin da yake amsa tambaya kan ko ƙawancen ya ɓoye wata adawa ta cikin gida tsakanin sansanonin biyu, Kwankwaso ya kafa hujjar cewa rashin jituwa tsakanin shugabanni da mataimakansu na faruwa ne sakamakon kwaɗayi, ba wai don tsarin tafiyar ba.

“Matsalar da mutane ke fuskanta, musamman shugabanni, ita ce sun cika kwaɗayi har ta kai ga sun fara samun sabani. Akwai ayyuka da dama da za a yi. Ba sai ka yaƙi mataimakinka ba."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya kare matakin aiki tare da Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya tuna baya

Ya bayyana cewa tarihin ayyukansa a matsayin tsohon mataimakin shugaban Majalisar wakilai, sannan kuma daga baya a matsayin gwamnan jihar Kano, ya nuna cewa haɗin gwiwar siyasa na iya dorewa koda kuwa akwai matsin lamba.

“Na samu damar yin aiki da shugaban majalisa kuma mun yi aiki sosai. Na yi shekaru takwas a Kano duk da wahalar da nake sha da mataimakin gwamnana na wancan lokacin. Mun samu damar yin aiki na shekaru takwas cikin lumana har ta kai ga na miƙa masa mulki."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya goyi bayan NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da matsayar jam'iyyar NDC kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna goyon bayansa ga matakin jam’iyyar na bai wa Kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Ya ce matakin zai bai wa yankin Kudu damar kammala wa’adinsa na jagorancin ƙasa cikin tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng