Gasar cin kofin nahiyar Afrika: Algeria ta sha da kyar a hannun Najeriya
Najeriya da kasar Algeria sun fito zagaye na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da ake buga awa a kasar Masar (Egypt).
Tuni aka kammala buga wasan zagayen nakusa da na karshe tsakanin kasar Senrgal da Tunisia, inda kasar Senegal ta samu nasarar fito wa zuwa wasan karshe bayan ta doke kasar Tunisia a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Yanzu haka kasar Senegal na jiran Najeriya ko Algeria a wasa na karshe da za a buga a gasar AFCON.
An take wasa tsakanin Najeriya da Algeria da misalin karfe 8:00 na dare a filin wasa da ke Cairo, babban birnin kasar Masar.
Minti na 9 zuwa 15: 'Yan wasan kasar Algeria; Belaili da Feghouli na yi wa Najeriya barazana ta hanyar yawan kutsa wa zuwa cikin gidan Najeriya.
Najeiya ta samu kwana a minti na 17 bayan ta samu shiga gidan kasar Najeria. Kenneth Omeruo ya saka mata kai amma ta yi yawa.
Akwai alamun rauni a bayan Najeriya. Dan wasan gaba na kasar Algeria Belaili na yawan matsa wa gidan Najeriya. Dan wasa Mahrez na cigaba da burge wa a bangaren raba kwallo.
Bayan fiye da mintuna 25 ana fafata wa, magoya bayan kasar Algeria ne ke murna da jin dadin yadda 'yan wasan kasar su suka takure Najeria.
Mintuna kusan 40 kenan ana taka leda, amma babu ci a wasan. Har yanzu kasar Algeria ce ta mamaye wasan da yawan mallakar kwallo da kai kora gidan Najeriya.
Dan wasan Najeriya William Troost-Ekong ya ci gida a minti na 40 daidai.
An tafi hutun rabin lokaci, kasar Algeria na da 1, Najriya 0.
An dawo daga hutun rabin lokaci, kasar Algeria na da 1, Najriya 0. Babu bangaren da ya yi canji yayin hutun rabin lokacin.
An bawa dan wasan Algeria, Bounedjah katin gargadi saboda yi wa dan wasan Najeriya, Iwobi, keta a minti na 51.
Har yanzu kasar Algeria ce ke taka leda, 'yan wasan Najeriya na taka leda da sanyin jiki, ba kamar yadda suka saba yi a wasanninsu na baya ba.
'Yan Najeriya a dandalin sada zumunta na rokon 'yan wasan Najeriya su mayar da hankali, su yi wasa da zuciyarsu musamman ganin cewa an wuce mintuna 60 ana fafata wa.
An bawa dan wasan kasar Algeria Feghouli katin gargadi, an bawa Najeriya bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan an tuntubu na'ura (VAR).
Ighalo ya farke wa Najeriya a daidai minti na 72. Algeria na da 1, Najeriya na da 1, an yi kunnen doki.
An ketara mintuna 80 ana buga wasa, kasa da mintuna 10 a cinye lokacin wasan. Har yanzu ana tafiya kunnen doki tsakanin Algeria da Najeriya.
'Yan wasan Najeriya sun samu karin karfi bayan Ighalo ya farke kwallon da aka zira musu.
Maharez ya ci Najeriya a daidai lokacin da wasa ya kare. Algeria 2, Najeria 1.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng