Hatta Dangote sai da tarin talauci da ke karkashin mulkin Buhari ya shafe shi - Atiku
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan ba a yi hankali ba, ga baki daya yan Najeriya zasu fada cikin talauci.
Yayin da yake bayyana ra’ayinsa akan rahoton kungiyar shirin ci gaba na majalisar dinkin duniya (UNDP), wanda ke nuna cewa yan Najeriya miliyan 98 sun kasance cikin talauci, Atiku yace hatta Aliko Dangote, mai arzikin Afirka sai da talaucin dake cigaba da yaduwa a kasar ya taba shi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi “wadanda suka saka Najeriya cikin wannan halin a matsayin marasa kishi, inda ya kara da cewa barazana akan tsaron da kasar ke fuskanta a halin yanzu ba lamarin Boko Haram ko yan bindiga bane, illa kasancewar kasar ta tsunduma cikin tarin talauci a tarihi.
Yayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su hada hannu don neman mafita akan lamarin.
“Gazawar tattalin arzikinmu a cikin shekaru hudu da suka gabata ya shafi kowa daga sama har zuwa kasa. Shekaru hudu da suka gabata, Aliko Dangote, mai kudin Najeriya da Arika ya mallaki $25bn. Sai dai kuma, a 2019 ya mallaki kasa da haka.
KU KURANTA KUMA: Allah ya kyauta: Bokan mu ne yace mu yanko masa kayuwan 'yan uwanmu zai bamu maganin samun kudi - Masu laifi
"Ya shiga sahun dubban yan kasuwa wadanda karfin samunsu ya ragu a yan shekarun da suka gabata kuma hakan ya cigaba da faruwa,” ya fadi hakan ne a wani jawabin da kakakinsa Paul Ibe ya gabatar a madadinsa.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng