Takarar 2027: Yusuf Buhari Ya Gana da Shugaban Majalisar Wakilai

Takarar 2027: Yusuf Buhari Ya Gana da Shugaban Majalisar Wakilai

  • Dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya kai ziyara ta musamman ga Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen
  • Yusuf Buhari ya sanar da cewa ya kai ziyara ga shugaban majalisar ne tare da wasu abokan shi kuma ganawar ta yi kasance mai cike da fa'ida
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi tsokaci kan ganawar Yusuf Buhari da Abbas Tajudeen, inda wasu ke cewa ya kamata ya cigaba da shiri sosai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yusuf Buhari ya bayyana godiyarsa ga shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas bayan wata ziyarar girmamawa da ya kai ofishinsa da ke harabar majalisar dokoki ta ƙasa a Abuja.

A cikin wata sanarwa, Yusuf Buhari ya ce ya samu damar kai ziyarar ne da wasu abokansa, yana mai bayyana tattaunawar da suka yi a matsayin mai armashi, cike da fahimtar juna da kuma amfani.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da korafe korafe kan Buhari game da taimaka masa a 2015

Yusuf Buhari da Abbas Tajudeen
Yusuf Buhari na gaisawa da Abba Tajudeen a Abuja. Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Yusuf Muhammadu Buhari ya yi bayan ganawar ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Ganawar Yusuf Buhari da Tajuddeen Abbas

Bayan ganawa da shugagaban majalisar, Yusuf ya yaba masa bisa kyakkyawar tarba, karamci da kuma shawarwari masu amfani da ya ba su.

Yusuf Buhari ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Abbas jagora da ƙarfafa shi wajen hidimtawa Najeriya, inda ya ce:

“A yau, na samu damar kai wasu daga cikin abokaina ziyarar girmamawa ga shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, a ofishinsa da ke harabar majalisar dokoki ta ƙasa a Abuja.
"Mun yi tattaunawa mai armashi da amfani kuma ina matuƙar gode masa bisa tarba, karamci da kalaman ƙarfafawa masu muhimmanci da ya yi mana.
"Allah Ya ci gaba da yi masa jagora da ƙarfafa shi wajen yi wa ƙasarmu mai daraja hidima.”

Kara karanta wannan

Takara: Kalaman Pantami sun tayar da kura, an shawarce shi kan zaman lafiya

Ra’ayoyin ’yan Najeriya

’Yan Najeriya da dama, musamman masu amfani da kafar sadarwa ta X, sun yi tsokaci bayan ziyarar da Yusuf Buhari da abokansa suka kai.

Ositadinma Okeke ya ce:

“Allah ba zai ƙarfafa shi ko wasu ba saboda su azzalumai ne kuma ba sa son yin abin da muka zaɓe su domin yi.”

Ozi-Anokehi ya ce:

“Addu’o’i na da goyon bayana suna tare da kai.”
Yusuf Buhari da abokan shi a wajen Abbas Tajudeen
Wasu abokan Yusuf Buhari tare da Abbas Tajudeen. Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

Alanposir Natureman ya ce:

“Lallai kai mutum ne da ya dace da shugabanci. Za su taimaka maka wajen cin nasara.
“Allah Maɗaukakin Sarki Ya kare ka, Ya kuma albarkace ka. Baba zai yi alfahari da kai.”

Adefolalu Adebodunde Sunday ya ce:

“Ka gina tafiyar ka a dukkan jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774... Ina ganin a nan gaba za ka cimma abin da ya fi burinka na yanzu.”

Yusuf Buhari ya nada hadimi

A wani labarin, mun kawo muku cewa dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da hada kan jama'a game da matsayi da zai nema a 2027.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi dalilin da ya sa ya zubar da hawaye kan takara a Borno

Yusuf Buhari ya nada Aliyu Haruna Daura a matsayin jagoran hulda da jama'a game da kamfen da zai yi domin neman kujerar majalisar wakilai.

Baya ga nada mukamai, dan tsohon shugaban kasar ya sanar da cewa ya gana da wasu daga cikin mutanen mazabar shi domin jin damuwowinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng