Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kano, Sun Kashe Bayin Allah

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kano, Sun Kashe Bayin Allah

  • 'Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Yankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano, inda suka kashe mutum biyar
  • Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, inda maharan suka fito daga maƙwabciyar jihar Katsina suka buɗe wuta ba kaukautawa
  • Shugaban ƙauyen Yankamaye, Sunusi Abubakar, ya tabbatar da cewa maharan sun sace adadi mai yawa na dabbobi kafin su tsere daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane biyar a ƙauyen Yankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Maharan, waɗanda ake zargin sun fito ne daga jihar Katsina, sun far wa ƙauyen ne da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma a ranar Litinin, inda suka jefa mutane cikin fargaba.

Kara karanta wannan

Sun haura $29bn: Amurka ta fadi makudan kudaden da ta kashe a yaki da Iran

'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 5 a harin da suka kai Kano
Hanyar shiga karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano. Hoto: Tsanyawa Kano
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kano

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa ƴan bindigan sun riƙa harbi ba kaukautawa, lamarin da ya sa mutane tserewa domin tsira da rayukansu, in ji rahoton Premium Times.

Shugaban gargajiya na ƙauyen Yankamaye, Sunusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, 12 ga Mayu, 2026. A cewarsa:

"Sun zo ne da yamma suka fara harbi ba tare da kakkautawa ba. Waɗanda suka gudu daga gidajensu domin ɓoya a daji su ne suka fi zama abin farmaki. Mutum biyar aka kashe, wasu huɗu kuma sun ji rauni, sannan an sace shanu masu yawa."

Jagoran ƙauyen ya ƙara da cewa jami'an tsaro na haɗin gwiwa da ke zaune a hedikwatar ƙaramar hukumar Tsanyawa sun isa wurin jim kaɗan bayan maharan sun tsere zuwa kan iyakar jihar Katsina da dabbobin da suka sace.

Martanin 'dan majalisa kan wannan hari

Hon. Sani Bala Tsanyawa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ghari/Tsanyawa, ya tabbatar da harin a shafinsa na Facebook inda ya bayyana sunan ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin sojojin sama ya kashe kusan mutane 100 a Zamfara

'Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Kano.
Taswirar jihar Kano, inda 'yan bindiga suka kashe mutane 5 a Tsanyawa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ɗan majalisar ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai da dangin waɗanda abin ya shafa, tare da addu'ar samun sauƙi ga waɗanda ke karɓar magani a asibiti.

"Innalillahi Wainna'inna ilaihi rajiun. Allah ka kawo ma Yankamaye sauki, Allah ka shiga lamarin Yankamaye.
"Ya zuwa yanzu an samu gawar mutum uku da 'yan bindiga suka kashe sakamakon shigar su Yankamaye da magribar nan. Allah ya jikansu ya yi masu gafara.
"An kawo labarin tsintar gawar Nasiru Bawale a bayan gari, ya zama mutum na biyar da aka kashe kuma hudu na asibiti. Allah ya gafarta masu."

- Hon. Sani Bala Tsanyawa.

'Yan bindiga sun yi kisa a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mainika da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, inda suka kashe wani makiyayi.

Kansilan Mainika, Auwal Abdussalam Barau, ya bayyana cewa maharan sun zo ɗauke da mugayen makamai, kuma ana zargin sun shigo ne daga jihar Katsina.

Auwal Barau ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta duba yiwuwar kafa sansanin soja a yankin domin dakile hare-haren da ake kai wa al’ummar yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com