Alex Ekubo: Fitaccen Jarumin Fina Finan Najeriya Ya Mutu Yana da Shekaru 40

Alex Ekubo: Fitaccen Jarumin Fina Finan Najeriya Ya Mutu Yana da Shekaru 40

  • Shahararren jarumin Nollywood, Alex Ekubo, ya rasu a ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026, bayan ya shafe watanni yana fama da jinya
  • Abokan aikinsa irin su Funke Akindele da Bolanle Ninalowo ne suka fara sanar da rasuwarsa a shafukansu na sada zumunta
  • Kafin rasuwarsa, jarumin ya yi watanni ba ya fita a bainar jama'a, wanda hakan ya tada wa magoya bayansa hankali tun a ƙarshen 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Masana'antar fina-finai ta Najeriya, Nollywood, ta shiga yanayin makoki bayan samun labarin rasuwar fitaccen jarumi Alex Ekubo.

Jarumin, wanda ya yi fice wajen fitowa a fina-finan ban dariya da na soyayya, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 40.

Fitaccen jarumin Nollywood, Alex Ekubo ya rasu
Fitaccen jarumin Nollywood, Alex Ekubo da ya rasu a ranar 11 ga Mayun 2026. Hoto: @AlexxEkubo/X, Diy13 via Getty Images.
Source: UGC

Fitaccen jarumin Nollywood ya rasu

Labarin mutuwar tasa ya bazu ne a ranar Talata, 12 ga Mayu, 2026, bayan abokan aikinsa sun fara wallafa saƙonnin ban-kwana, kamar yadda jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin sojojin sama ya kashe kusan mutane 100 a Zamfara

Fitacciyar jaruma Funke Akindele ta bayyana cewa:

"Hmmmmmm. Ubangiji ya jikanka Alex. Na yi ƙoƙarin tuntuɓarka domin mu sake yin magana a karo na ƙarshe, amma kadara ta riga fata. 'Ore mi' (kawata) kamar yadda kake kirana, zan ci gaba da tunawa da kyawawan lokutan da muka shafe tare."

Shima jarumi Bolanle Ninalowo, wanda ke ƙasar Amurka a halin yanzu, ya taya iyalan jarumin alhini inda ya ce:

"Ubangiji ya jikanka Alex. Ubangiji ya ba iyalinka da mu duka haƙurin wannan rashi."

Ekubo ya janye daga fim kafin mutuwarsa

Tun a watan Disamba na shekarar 2024 ne Alex Ekubo ya daina wallafa komai a shafinsa na Instagram, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce game da halin da yake ciki, in ji rahoton Punch.

Ko da yake wasu abokansa irin su Stanley Ontop sun taɓa fitowa a 2025 sun ce jarumin yana nan lafiya kuma ya ɗauki hutu ne kawai, amma wani bidiyo da ya karade gari kwanan nan ya nuna jarumin ya rame sosai.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari

Rahotanni sun bayyana cewa jarumin ya yi fama da ciwon kansa na tsawon watanni, wanda hakan ya sanya shi janyewa daga harkokin fim da na jama'a.

Godwin Nnadiekwe, wanda makusancin jarumin ne, ya bayyana cewa abin ya girgiza shi sosai:

"Wannan labari ya karya mini zuciya. Nollywood ta rasa babban mutum, abin takaici ne matuƙa."
An ce Alex Ekubo ya fara shahara a Nollywood ne a shekarar 2010.
Fitaccen jarumin Nollywood, Alex Ekubo da ya rasu. Hoto: @AlexxEkubo
Source: Instagram

Ayyukan Alex a Nollywood

Alex Ekubo ya fara fice ne a shekarar 2010 bayan ya zama na biyu a gasar Mr Nigeria. Daga nan ya zama ɗaya daga cikin jaruman da suka fi tasiri a Afrika baki ɗaya.

Ya fito a fina-finai kamar Weekend Getaway, Sugar Rush, da Merry Men, kamar yadda rahoton Radio Nigeria.

Ko da yake bai taɓa yin aure ba kafin mutuwarsa, rayuwarsa ta kasance mai cike da nasarori a fagen wasan kwaikwayo da samun lambobin yabo.

Iyalansa ba su riga sun fitar da cikakkiyar sanarwa kan shirye-shiryen jana'iza ba, amma masana'antar fim ta riga ta fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan karrama shi.

Jarumin fim ya rasu yana barci

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: Hotuna sun nuna yadda mutane fiye da 15 suka mutu a hanyar Kogi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jarumin fina-finan Nollywood, Solomon Akiyesi ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Iyalansa sun bayyana cewa ya kwanta barci bayan ya fara shan maganin gyambon ciki, amma da safe aka tarar da gawarsa a Abuja.

Shugaban kungiyar AGN, Yakub Abubakar ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masana’antar fina-finai ta Nollywood.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com