Wasan Najeriya da Algeria: Sanata Ahmed Lawan ya tafi kasar Masar

Wasan Najeriya da Algeria: Sanata Ahmed Lawan ya tafi kasar Masar

A yayin da a daren yau na Lahadi 14, ga watan Yuli, za a fafata tsakanin Najeriya da kuma kasar Algeria a zagaye na biyu karshen na gasar kofin nahiyyar Afirka AFCON, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya zuwa kasar Masar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Ahmed Lawan, ya jagoranci tawagar shugaban kasa domin jaddada goyon baya ga 'yan wasan kwallon kafa na kasar nan a yayin wasan da za su kara tsakanin su da na kasar Algeria a gasar kofin nahiyyar Afirka da ake fafatawa a kasar Masar.

Mai magana da yawun shugaban majalisar dattawa, Muhammad Isa, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan tarayya.

Cikin jawaban da Sanata Lawan ya gabatar gabanin tafiyar sa, ya ce kasancewar tawagar gwamnatin tarayyar kasar nan zai kara kaimi na karsashi da kuma karfin gwiwa ga 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya yayin da za fafata wannan babban wasa da samun nasarar sa ke da matukar muhimmanci.

A yayin da yake tabbatar da muhimmancin goyon bayan gwamnatin tarayya a kan 'yan wasan kwallon kafa na kasar nan, shugaban majalisar dattawan ya kyautata zato gami da sa ran a kan cewa Najeriya za ta lashe gasar AFCON na bana.

Tawagar gwamnatin tarayya da ta kunshi mutane 11 da tayi tattaki zuwa kasar Masar ta hadar da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

KARANTA KUMA: Zaben 2023: Mulkin Najeriya zai ci gaba da kasancewa a Arewa - Unongo

Sauran 'yan tawagar sun hadar da gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele, shugaban kwamitin wasannin Olympic na Najeriya, Habu Gumel da kuma wakilin fadar shugaban kasa, Kaftin Hosa Okunbo.

Kazalika tawagar ta hadar da sakataren dindindin na ma'aikatar wasanni da matasa, Olusade Adesola, daraktan ma'aikatar wasanni, Muhammad Gambo da kuma tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel