Zaben 2023: Mulkin Najeriya zai ci gaba da kasancewa a Arewa - Unongo
- Paul Unong ya tsarkake babban zaben kasa na 2019 fiye da 1993
- Tsohon Ministan ya ce Arewacin Najeriya yana da duk wata cancanta ta ci da rike mulkin kasar nan a zaben 2023
- Tsohon shugaban kungiyar dattawan Arewa ya ce Shugaban kasa Buhari ya samu aminci a Arewa
Tsohon minista kuma tsohon shugaban kungiyar dattawan Arewa, Paul Unongo, ya yi hasashe tare da kyautata zato a kan Arewacin Najeriya wajen samar da shugaban kasa tare da ci gaba da rike akalar jagoranci a zaben 2023.
Dattijon na kasa ya bayyara hakan ne yayin wata hira da manema labarai na jaridat The Sun. Ya ce Arewacin Najeriya ke da mafi kololuwar cancanta ta ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar nan a 2023.
Unongo ya ce babban zaben kasa na 2019 ya tsarkaka cikin gaskiya da kuma adalci fiye da yadda ta kasance a babban zabe na 1993 a yayin da mafi rinjayen kaso na al'ummar kasar nan suka kadawa shugaba Buhari kuri'u wajen tabbatar da nasarar sa.
Cikin kalami na sa, Unongo ya ce "fiye da kaso 80 cikin 100 na talakawan kasar nan sun shimfida aminci da kuma dogara a kan shugaban kasa Buhari tamkar wani abun bauta da ba za su taba juya masa baya ba."
A yayin da dimokuradiyya ke ci gaba da samun gindin zama a kasar nan, mulkin Najeriya zai ci gaba da kasancewa a Arewa a yayin zaben 2023 duba da mafi rinjayen kaso na adadin al'umma a yankin."
KARANTA KUMA: Hatsarin mota ya kashe sabuwar amarya da mutane 4 a jihar Ogun
Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa na zaben 12 ga watan Yunin 1993 a karkashin inuwa ta jam'iyyar SDP, Dr Uma Eleazu, ya debe tsammani da cewar akwai yiwuwar za a shafe babin Najeriya daga doron kasa a 2023.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng