Adamawa: Jama'ar wani gari a Mayo-Balwa sun mayar da Masallaci Asibiti

Adamawa: Jama'ar wani gari a Mayo-Balwa sun mayar da Masallaci Asibiti

Al'ummar garin Wuro Ahmadu da ke yankin gandun daji na Gongoshi a karamar hukumar Mayo-Belwa, jihar Adamawa, sun mayar da Masallacinsu Asibiti saboda tsanani bukatar wurin da za a ke duba lafiyarsu.

Garin Wuro Ahmadu tamkar ruga ce ta Fulani makiyaya da ke da mutane da yawansu ya kai 1,000 da dabbobi fiye da 20,000.

Maigarin yankin, Ardo Buba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi cewa sun yanke shawarar mayar da Masallacin asibiti ne saboda tsananin bukatar wurin da za a ke duba lafiyarsu.

"Mu na da jama'a fiye da 1,000 a garin Wuro Ahmadu da kewaye. Amma duk lokacin da wani bashi da lafiya ko idan mai juna biyu ta fara nakuda, sai mun yi tafiyar fiye da sa'a guda kafin mu iske asibiti.

"Mun shafe fiye da shekara 10 a cikin wannan mawuyacin hali, amma babu wanda ya nuna zai taimake mu. Don haka ne muka yanke shawarar sadaukar da Masallacin mu ya koma asibiti," a cewar Buba.

Ya roki gwamnati da ta taimake su da kayan aikin duba lafiya, da magunguna da kuma ma'aikatan da zasu ke duba lafiyar jama'a.

Ya kara da cewa jama'ar yankin na bukatar makarantar da yaransu zasu ke zuwa da kuma asibiti na gaske da za a ke kwantar da marasa lafiya domin rage yawaitar mutuwar mutanen garin.

Buba ya kara da cewa hatta ruwan shan da suke amfani da shi wata kungiyar aikin jin kai ce ta gina musu rijiya (borehole) guda biyu domin amfaninsu da dabbobinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel