'Yan daban daji sun salwantar da rayuka 10, sun raunata mutane 5 a jihar Katsina

'Yan daban daji sun salwantar da rayuka 10, sun raunata mutane 5 a jihar Katsina

Tabbas rayukan mutane 10 sun salwanta kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana a sakamakon wani mummunan hari na 'yan daban daji da ya auku a kauyen Kirtawa na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kazalika wannan mummunan hari ya raunata kimanin mutane biyar a jihar Katsina da ta kasance mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Masu ta'adar sun kuma kone kimanin motoci biyar da kuma babura hudu tare da satar dumbin shanu yayin aukuwar wannan hari.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, shi ne ya bayar da tabbacin wannan mummunan lamari yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi 14, ga watan Yulin 2019.

KARANTA KUMA: Jinkirin nadin ministoci ya jefa ma'aikatu 3 na gwamnatin Tarayya cikin kunci

SP Gambo ya kuma bayar da tabbacin jikkatar wani jami'i daya na hukumar dakarun soji kasa da kuma na hukumar NSCDC yayin artabu da masu tayar da zaune tsaye.

Yayin jajantawa 'yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, babban jami'in na hukumar ta damara, ya ce 'yan daban daji fiye da 300 ke da alhakin kai wannan mummunan hari da misalin karfi 5.20 na Yammacin ranar Asabar da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel