RHA Ta Kafa Hujjoji, Ta Ce Shugaba Tinubu Ya Cika Alkawurran da Ya Daukar wa 'Yan Arewa

RHA Ta Kafa Hujjoji, Ta Ce Shugaba Tinubu Ya Cika Alkawurran da Ya Daukar wa 'Yan Arewa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cika duk alkawurran da ya daukar wa mutanen Arewa a lokacin yakin neman zaben 2023
  • Kungiyar RHA ce ta bayyana hakan bayan ta kai rangadin duba ayyyukan gwamnatin Tinubu a shiyyar Arewa maso Yamma
  • RHA ta yi ikirarin cewa babu yankin da ya samu ayyukan raya kasa masu yawa kamar Arewa maso Yamma, tana mai cewa Tinubu ya cika alkawari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ƙungiyar magoya bayan Tinubu ta Renewed Hope Ambassadors (RHA) ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗaukar wa Arewacin Najeriya.

Kungiyar yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya cika alkawurran da ya dauka lokacin yaƙin neman zaɓe, ta hanyar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa a faɗin yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya gaza cika alkawari a Arewa?

RHA ta ce zargin da wasu ke yi na cewa shugaban ya gaza cika wa Arewa alƙawari ba shi da tushe ballantana makama, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar kungiyar ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa karkashin manufar "Renewed Hope Agenda" sun ƙaryata wannan zargi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan kammala rangadin gani da ido kan ayyukan Gwamnatin Tarayya a shiyyar Arewa maso Yamma.

RHA ta kai ziyara wasu yankunan Arewa

RHA ta ce gwamnatin Tinubu ta nuna jajircewa wajen sauya fasalin Arewa ta hanyar dabarun ayyuka da ke matakai daban-daban na kammaluwa.

Rangadin ya haɗa da ziyartar wuraren ayyuka tun daga mahadar Zuba a Babban Birnin Tarayya (FCT), da ayyukan da ake yi a Kaduna, Kano, Jigawa, har zuwa jihar Kebbi.

A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Tunde Rahman ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da ayyuka na musamman guda 260 a faɗin ƙasar ta hanyar Ma’aikatar Ayyuka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Murtala Garo ya zama sabon mataimakin gwamnan Kano

Ya ce daga cikin wadannan ayyuka shiyyar Arewa maso Yamma kaɗai ke da ayyuka 48 da ake gudanarwa, wanda hakan ya sa yankin ya fi ko'ina samun ayyuka a mulkin Tinubu.

Hujjojin da kungiyar RHA ta kawo

A lokacin rangadin duba aikin, tawagar ta ziyarci sassan babbar hanyar Abuja-Kaduna-Kano, wacce ake sake ginawa tare da fasahar shimfida titin kankare da kuma fitilun masu amfani da hasken rana.

A ruwayar Daily Post, RHA ta ce kashi na farko a aikin mai tsawon kilomita 82 ya kusa kammaluwa, kuma an tsara ranar kammala aikin baki ɗaya a watan Nuwamba na wannan shekara (2026).

Titin Abuja.
Wani sashen titin Abuja-Kaduna zuwa Kano da Ministan Ayyuka, Dave Umahi lokacin da ya je duba aikin Hoto: Dave Umahi
Source: Twitter

QƘungiyar ta kammala da cewa waɗannan ayyuka da sauran wadanda ake yi za su taimaka wajen sauƙaƙa sufuri, haɓaka kasuwanci da noma, da kuma samar da saurin bunƙasar tattalin arziƙi a Arewa.

Dalilin da zai sa a sake zaben Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya mayar da fom ɗin neman tsayawa takara na shugaban ƙasa a madadin Bola Tinubu.

A wani taro da aka yi a Abuja, Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027 domin a cewarsa ya kawo cigaba.

Shettima ya ce kokarin da Tinubu ya yi a zangon farko kadai zai sa yan Najeriya su zake mara masa baya a babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262