A yanzu haka matata na aure da wani makwabcinmu, mijin matar ya fadawa kotu

A yanzu haka matata na aure da wani makwabcinmu, mijin matar ya fadawa kotu

-Wani mutum ya bayyanawa kotu dalilin da ya sanya shi ya tsani matarsa

-Mutumin mai suna Hakeem Yusuf ya ce matar tasa bata halayya mai kyau ne kuma ta dade tana ha'intarsa domin tun kan su yi aure ta mashi karyar cewa ta na da ciki

-Hakeem ya ba kotun labarin cewa matar tasa ta aure wani makwabcinsa na kut da kut a halin yanzu

Wani magidanci mai suna Hakeem Yusuf wanda ke sana’ar tukin mota bas a garin Ibadan ya shaidawa kotun gargajiya ta Mapo dalilin da ya sa shi yake jibgar matarsa.

Matar ta sa mai suna Ronke, a cewar Hakeem tana ha’intarsa a cikin zamantakewarsu ne ta aure. Hakeem ya antayo wannan jawabin ne gaban alkalin kotun, Ademola Odunade a sanadiyar kararsa da matar ta kai na cewa ya na nuna mata uquba don haka take so a raba auren.

KU KARANTA:An ci Facebook tarar dala biliyan biyar ($5bn)

Hakeem wanda yake martani a kan saki da matar ta sa ta nema a kotun, ya ce ya auri matar ne shekaru goma da suka wuce inda a wan can lokacin yake tunanin cewa mutuniyar kirkice ashe kwanko ce bai sani ba.

“ Ni da Ronke mun kasance abokan juna ne gabanin mu yi aure, a hankali ta shammace ni har na aureta.

“ Karya ta yi mani a wai tana da ciki, bayan na aureta na fahimci cewa karya ce kawai ta sharara mani. Ko kadan Ronke ba matar aure bace ga duk mutum na kirki, ina sane da duk irin miyagun abubuwan da take aikatawa.

“ In takaice maku zance dai, a yanzu haka Ronke ta auri wani makwabcina na kut da kut. Abinda ke daure min kai shi ne babu wani abun da na rageta da shi.” A cewar Hakeem.

Ita kuma matar tasa a nata jawabin cewa tayi: “ Zargi ne kawai da tsananin kishi ya sanya mijina yake muzguna min amma ba wani abu nake aikatawa ba.”

Bayan alkali ya gama sauraron bangarorin biyu, sai ya ce “ abu mafi kyawo garesu shi ne a raba aurensu saboda babu so da qauna a tsakaninsu yanzu, saboda idan har suka samu haihuwa matsalar zata kara girmama.”

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ne ya samar mana da wannan labari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel