Nikakken tumatir mai dauke da guba ya shigo Najeriya daga kasar Iran - Hukumar Kastam

Nikakken tumatir mai dauke da guba ya shigo Najeriya daga kasar Iran - Hukumar Kastam

Hukumar hana fasa kauri ta kasa ta yi gargadin cewa, kwantenoni shida cike makil da nikakken tumatir mai dauke da guba ya shigo Najeriya daga kasar Iran da aka killace shi da sunan 'Shirin Asal my tomato paste'.

A sanadiya wannan mummunar barazana hukumar kasta take gargadi na hattara tare da ankarar da al'umma da kuma sauran hukumomin tsaro a kan dakile shigar wannan gurabataccen tumatir cikin kasuwannin kasar nan.

Rahotanni kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, kwantenoni shida masu dauke da wannan gurbataccen tumatir sun iso tashohin ruwa na kasar a wani babban tarago mai sunan Investment Limited.

Hukumar hana fasa kauri tare da hadin gwiwar hukumar tsaftace kayan abinci da magunguna ta NAFDAC, na neman hadin kan sauran hukumomin tsaro wajen dakila afkawar wannan gurbataccen tumatir cikin kasuwanni a fadin Najeriya.

A wani rahoton na daban da jaridar BBC Hausa ta wallafa a ranar 6 ga watan Maris na 2017, wata babbar Darkta a hukumar lafiya ta duniya, Margaret Chan, ta yi gargadin cewa gurbacewar iska na daya daga cikin babbar barazana ga lafiyar al'umma a doron kasa.

KARANTA KUMA: INEC ta fara shirin babban zaben kasa na 2023 - Yakubu

A hirar da ta gabatar, Margaret ta ce gurbatacciyar isakar da ake shaka ta fi illa ga lafiyar al'umma a kan cutar Ebola da kuma cuta mai karya garkuwar jikin dan Adam wato HIV. Haka zalika ta fi illa musamman a kan matasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng