Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde Zai Ayyana Shiga Takarar Shugaban Kasa a 2027

Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde Zai Ayyana Shiga Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • Gwamna Seyi Makinde zai kaddamar da neman takarar shugabancin kasa na 2027 a wani babban taro a dandalin Mapo Hall cikin makon nan
  • Taron zai zama dandalin bayyana sabon kawance tsakanin jam'iyyar PDP da APM, wanda Makinde da magoya bayansa ke jagoranta
  • Sai dai, bangaren Nyesom Wike ya fito ya musanta wannan kawance na PDP da APM, tare da zargin cewa an shirya batun don bata shirin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya shirya tsaf domin ayyana aniyarsa ta neman kujerar shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar 2027.

Wannan gagarumin taro, wanda aka yi wa laƙabi da “Unity Mega Rally Ibadan 2026”, zai gudana ne a dandalin Mapo Hall da ke birnin Ibadan a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Gwamna Seyi Makinde zai ayyana shiga takarar shugaban kasa.
Gwamna Seyi Makinde a wajen wani taron jam'iyyar PDP. Hoto: @seyimakinde
Source: Twitter

Makinde zai ayyana takarar shugaban kasa

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa jaridar Vanguard cewa an kammala shirye-shiryen taron yayin da magoya bayan gwamnan ke ta fadi-tashi wajen ganin an yi abin da ya kamata.

Wannan mataki zai zama silar buɗe sabon babi na tafiyar siyasar gwamnan wanda ya daɗe yana jan zare a yankin Kudu-Maso-Yamma.

Wasu majiyoyi sun bayyana wa jaridar cewa:

"Wannan taro zai kasance matattarar jagororin siyasa, kungiyoyin matasa, da kuma shugabannin al'umma daga sassan kasar nan wadanda ke goyon bayan salon mulki da hangen nesa na Gwamna Makinde.
"A wannan taron ne Gwamna Makinde zai kawo karshen shirun da ya yi na kudurinsa kan neman takarar shugabancin Najeriya."

2027: PDP da APM za su kulla kawance

Babban abin da zai fi ɗaukar hankali a taron na ranar Alhamis shi ne bayyana kawance na musamman tsakanin jam'iyyar PDP da kuma jam'iyyar APM.

Wannan na zuwa ne sakamakon rarrabuwar kawuna da aka gaza warwarewa a cikin uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa, wanda hakan ya sa Makinde da mutanensa fara neman madadin da zai ba su damar taka rawar gani a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Guguwa mai karfin gaske ta hallaka mutane, ta lalata gidaje fiye da 1200 a Borno

Ko da yake Gwamna Makinde bai riga ya fito fili ya furta cewa zai tsaya takara ba, amma ƙungiyoyin goyon baya da abokan arziƙinsa sun daɗe suna matsa masa lamba.

Idan Makinde ya samu tikitin takara, zai kara da Tinubu a zaben 2027.
Gwamna Seyi Makinde ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa. Hoto: @seyimakinde
Source: Twitter

PDP tsagin Wike ta karyata alaka da APM

A hannu daya, jaridar Tribune ta ruwaito cewa, ɓangaren Nyesom Wike na jam'iyyar PDP a jihar Legas ya karyata duk wani rahoto na kawancensu da APM.

Muka Popoola, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas wanda ke goyon bayan Wike, ya bayyana cewa:

"Waɗannan rahotanni na cewa jam'iyyar PDP ta ƙulla kawance da APM ƙarya ne kuma an shirya su ne domin yaudarar mutane.
"Waɗanda ke ruruta wutar wannan kawance tsofaffin mambobin jam'iyya ne da suka daɗe suna yi wa PDP zagon ƙasa."

Makinde ya tabo batun barin PDP

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Seyi Makinde, ya yi magana kan batun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ko wata jam'iyya daban.

Gwamna Makinde ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa zai fice daga PDP, inda ya bayyana cewa yana nan daram kuma yana jin daɗin zamansa a jam’iyyar adawa.

Gwamna Makinde ya yi jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com