Ana tsaka da Yakin Isra’ila da Iran, Girgizar Kasa Ta Afkawa Birnin Tehran
- Hukumomi a Jamhuriyar Iran sun tabbatar da samun girgizar kasa mai karfin maki 4.6 ta afku kusa da Tehran a kasar
- Hukumar binciken girgizar kasa ta Iran ta bayyana cewa girgizar ta auku ne kusa da iyakar Tehran da Mazandaran
- Rahotanni sun ce an ji girgizar a wasu yankuna da birane makwabta, amma har yanzu ba a samu bayanan asarar rayuka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Wata girgizar kasa mai karfin maki 4.6 ta afku kusa da birnin Pardis da ke gabashin Tehran a kasar Iran da daren Talata 12 ga watan Mayun 2026.
Cibiyar kula da girgizar kasa ta Iran ta bayyana cewa girgizar ta faru da misalin karfe 8:16 na dare agogon GMT a zurfin kilomita 10.

Source: Getty Images
An samu girgizar kasa a Iran
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa cibiyar girgizar tana kusa da iyakar lardunan Tehran da Mazandaran, kimanin kilomita 41 daga Tehran da 77 daga Karaj.
An kuma bayyana cewa an ji girgizar a wasu yankuna da dama, musamman gabashin lardin Tehran da wasu birane makwabta a Mazandaran.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da bayanan samun asarar rayuka ko barnar dukiyoyi sakamakon girgizar kasar ba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya jawo fargaba tsakanin mazauna yankunan da girgizar ta shafa, musamman wadanda ke kusa da babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Masana sun ce girgizar kasa irin wannan na iya haddasa tashin hankali a yankunan da ke kusa da cibiyar girgizar duk da cewa ba ta da tsananin yawa.
Kasar Iran na daga cikin wuraren da ake yawan samun girgizar kasa saboda kasancewarta a yankin da ke fama da motsin kasa.

Source: Getty Images
Ana ci gaba da bibiyar lamarin a Iran
Hukumomin kasar sun ce suna ci gaba da bibiyar halin da ake ciki domin tabbatar da ko akwai wata matsala da ta biyo bayan girgizar, cewar rahoton Anadolu Ajansi.
An shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa su kasance cikin shiri tare da bin umarnin hukumomi idan aka samu wani sabon gargadi.
Hukumar sadarwa ta Iran ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ta wallafa a shafin X a daren Talata 12 ga watan Mayun 2026.
Sanarwar ta ce:
An sanya jami’an agajin 'Red Crescent Society of the Islamic Republic of Iran' a cikin lardunan Tehran, Mazandaran, Qom da Alborz cikin shirin ko-ta-kwana.
"Sa’a guda bayan girgizar kasar, ba a samu rahoton jikkata mutane ba, kuma da alama babu wata babbar asarar dukiya da aka samu."
Girgizar kasa ta faru a Iran a 2025
A baya, mun ba ku labarin cewa girgizar ƙasa mai karfin 5.2 ta faru a tsakiyar Iran yayin da ƙasar ke ci gaba da musayar wuta da Isra'ila tun makon da ya gabata.
Rahotanni sun nuna cewa duk da girgizar kasar ba ta zurfi a cikin ƙasa ba amma lamarin ya ƙara jefa jama'a a cikin fargaba da tashin hankali mai tsanani.
Tun ranar Juma'a 16 ga watan Yunin 2026, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke fama da hare-hare daga Isra'ila, sannan aka ci gaba a ranar 28 ga watan Afrilun 2026, lamarin da ya ƙara dagula sha'anin taaro a Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

