Kwankwaso Ya Fadi Mutanen da Suka Mika Sunansa ga Majalisar Amurka kan Zargin Ta'addanci
- A kwanakin baya sunan madugun Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya je Majalisar dokokin Amurka kan zargin take 'yancin addini
- Ana dai zargin Kwankwaso da take 'yancin addini a lokacin da yake gwamnan Kano ta hanyar bullo da Shari'a, inda aka ba da shawarar a kakaba masa takunkumi
- 'Dan takarar shugaban kasar a zaben 2023, ya nuna kwarin gwiwar cewa kudirin ba zai tsallake ba domin ko kadan babu kamshin gaskiya a zargin da ake yi masa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan zargin da ake masa a Amurka kan take 'yancin addini.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa wasu makiyansa ne daga nan gida Najeriya suka mika sunansa ga majalisar dokokin Amurka.

Source: Facebook
Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.
Sunan Rabiu Kwankwaso ya je Majalisar Amurka
A kwanakin baya, wasu 'yan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore da Chris Smith, sun gabatar da wani kudirin doka mai suna Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026.
A cikin kudirin da suka gabatar, 'yan majalisa sun bayar da shawarar kakaba takunkumi kan wasu ’yan Najeriya ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso da kungiyoyi.
Kudurin ya ba da shawarar a kakaba takunkumi na musamman, da suka hada da daskarar da kadarori da hana biza ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso a kan zargin da ake yi masa
Lokacin da aka tambayi Kwankwaso kan yadda aka yi sunansa ya je majalisar Amurka, sai ya ka da baki ya ce:
"Eh ban sani ba, amma akwai jita-jita mai yawa cewa makiyanmu a nan Najeriya ne suka mika sunan. Na san cewa ba abokina ba ne ya mika sunan."
"Amma a karshe dai majalisar Amurka ba sakarkaru ba ne, za su yi bincike kuma za su gane cewa suna zargin mutumin da ba shi da laifi."
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Facebook
Kudirin ba zai tsallake ba - Kwankwaso
Dangane da ko zargin da ake yi wa Kwankwaso a Amurka zai iya lalata siyasarsa a gida Najeriya da waje, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa kudirin ba zai yi nasara ba.
"Ina da cikakken kwarin gwiwar cewa kudirin ba zai tsallake ba, za su yi bincike, ba gaskiya ba ne, ba daidai ba ne, kuma tabbas ba zai yi nasara ba."
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Kwankwaso ya magantu kan aiki da Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan yiwuwar yin aiki tare da Atiku Abubakar a 2027.

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya
Kwankwaso ya bayyana cewa shi da Atiku Abubakar har yanzu za su iya yin aiki tare kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ya raba gari da jam'iyyar ADC ne bayan ya fahimci cewa tana da tarin matsaloli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

