Mu na da mutum 378 da za su bada shaida a game da zaben Kano - Lauyan PDP

Mu na da mutum 378 da za su bada shaida a game da zaben Kano - Lauyan PDP

Jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kano, ta bayyana shirin ta na kiran shaidu fiye da 300 da za su gabatar da tarin hujjoji a game da zaben gwamnan jihar Kano da a ka yi a watan Maris na 2019.

Shugaban Lauyoyin da ke kare jam’iyyar PDP a gaban kotu, Adegboyega Asiwaju Awomolo SAN, ya bayyana wannan a lokacin da ya kira wani taron Manema labarai a kotun da a ke shari’a.

Babban Lauya AdegboyegaAwomolo ya ke cewa su na da mutane har 378 da za su bayyana a gaban kotu domin bada shaida a kan yadada a ka tafka magudi a zaben gwamnan jihar Kano.

A na ta bangaren, hukumar zabe ta kasa watau INEC ta fara shirin kare kan ta a gaban kotu da masu bada shaidan ta inda ta ke kokarin gamsar da kotu cewa an yi zaben kwarai a jihar Kano.

KU KARANTA: Yadda zaben Kano ya kasance tsakanin Ganduje da Abba Gida-Gida

Babban Lauyan da ke kare hukumar zaben, Ahmed Raji Saka SAN ya ce su na da mutanen 29 da za su bada shaida. A cikin makon nan ne kotu za ta cigaba da zama domin sauraron shari’ar.

Gwamnan jihar Kano mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya tanadi wadanda za su bada shaida har mutum 203 kamar yadda Lauyan da ke karesa watau Offiong Offiong SAN ya bayyana.

Ita ma jam’iyyar APC mai mulki wanda ta na cikin wadanda a ke tuhuma, ta na da masu bada shaida a gaban kotu har mutane 300 inji babban Lauya mai kare APC, Christopher Oshiomole.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu

:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel