Zaben 2027: Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus Ya Ayyana Shiga Takarar Gwamna a Oyo

Zaben 2027: Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus Ya Ayyana Shiga Takarar Gwamna a Oyo

  • Tsohon ministan wuta, Adebayo Adelabu, ya ƙaddamar da neman takarar gwamnan Oyo a zaɓen 2027 a dandalin wasanni na Obafemi Awolowo
  • Idan ya ci zabe, Adelabu zai yi amfani da dabtarin "Sake Haifar Oyo" wanda ya zai inganta arziki, samar da ayyukan yi, da gyara tsarin mulki
  • Jiga-jigan jam'iyyar APC da dama ne suka halarci taron, inda Adelabu ya jaddada cewa haɗin kan mambobi shi ne kaɗai zai ba jam'iyyar nasara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Oyo - Tsohon ministan wuta, Chief Adebayo Adelabu, ya fito fili ya ayyana aniyarsa ta sake neman takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Adelabu, wanda tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ne, ya bayyana hakan ne a wani babban taro da ya gudana a dandalin wasanni na Obafemi Awolowo, Oke-Ado da ke birnin Ibadan.

Kara karanta wannan

Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde zai ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2027

Adebayo Adelabu ya ayyana shiga takarar gwamnan jihar Oyo
Tsohon ministan wuta, Adebayo Adelabu da ya ayyana shiga takarar gwamnan Oyo. Hoto: Bayo Adelabu
Source: Facebook

Tsohon minista ya ayyana takarar gwamna

A lokacin da yake jawabi, Parakoyi na ƙasar Ibadan ya bayyana cewa wannan yunƙuri ne na dawo da martaba da ci gaban jihar Oyo, in ji rahoton Arise News.

A cewarsa:

"Wannan aiki ya fi ƙarfin mutum ɗaya; manufa ce ta haɗin gwiwa. Dole ne mu haɗa kai, mu ɗinke ɓaraka, sannan mu fifita muradin jam'iyya da nasarar bai-ɗaya a kan burin kanmu."

Adelabu ya gabatar da wani tsari na musamman mai suna “Shirin Sake Haifar Oyo,” wanda ya bayyana a matsayin madubin ci gaban da zai bi idan har aka zaɓe shi.

Wannan tsari ya ƙunshi gyaran fuska ga harkar ilimi da kiwon lafiya, samar da tsaro na zamani, da kuma kawo sauyi a fannin noma domin tabbatar da wadataccen abinci a jihar.

Gogewar Adelabu a shirin mulkar Oyo

Bugu da ƙari, ya yi alƙawarin ƙarfafa ikon ƙananan hukumomi domin kai ci gaba ga talakawan karkara, in ji rahoton jaridar Independent.

Kara karanta wannan

Alex Ekubo: Fitaccen jarumin fina finan Najeriya ya mutu yana da shekaru 40

Tsohon ministan ya bayyana kansa a matsayin "shugaban da aka riga aka tsara mulkinsa," yana mai nuni da cewa gogewarsa a fannin ma'aikatun gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu za ta taimaka masa wajen fuskantar ƙalubalen da jihar ke ciki.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan APC irin su Alhaji Mufutau Adisa Gbayawu, Hon. Lekan Adeyemo, da Alhaji Abu Gbadamosi, waɗanda suka yi kira ga mazauna jihar da su mara wa Adelabu baya.

Adebayo Adelabu ya ayyana shiga takarar gwamnan Oyo
Dandazon mutanen da suka halarci taron kaddamar da takarar Adebayo Adelabu a Oyo. Hoto: Adelabu Support Agenda
Source: Facebook

Siyasar Oyo gabanin zaben 2027

Shugabannin sun nuna yaƙinin cewa kwarewar Adelabu a matsayin mai gudanarwa ita ce za ta sa ya zarce sauran masu neman takarar a cikin jam'iyyar.

Wannan sanarwa ta Adelabu ta zo ne a daidai lokacin da siyasar jihar Oyo ke ƙara zafi, yayin da jam'iyyun adawa ke ƙoƙarin tattaro kan jama'a gabanin zaben.

Ana kallon takarar Adelabu a matsayin wani babban ƙalubale ga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar, musammam da yanzu da hankalin Gwamna Seyi Makinde ya karkata kan takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com