Gwamnatin Borno Ta Faɗi Tarkon da Ta Ke Yi wa Tubabbun Boko Haram da Alkur'ani
- Gwamnatin Borno ta yi ƙarin haske game da shirin sako tubabbun yan ta'adda cikin al'umma wanda ya ke tayar da hankula
- Ta ce ana sanya tsofaffin ’yan Boko Haram yin rantsuwa da Alkur’ani bayan shirin gyaran hali domin hana komawarsu ta’addanci
- Gwamnatin ta bayyana cewa duk wanda ya mika wuya ya zama kafiri a idanun ’yan ta’adda idan ya koma daji bayan shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Gwamnatin Borno ta kwantar wa al'umma hankali game da sake sako tubabbun yan ta'adda cikin mutane.
Gwamnatin ta ce tana kokarin kan yiwuwar tsofaffin ’yan Boko Haram da aka gyara tunaninsu su komawa cikin al'umma.

Source: Original
Tubabbun Boko Haram: Matakan da gwamnati ke dauka
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Borno, Zuwaira Gambo, ta bayyana hakan yayin hira da yan jarida, cewar Vanguard.
Ta bayyana cewa daya daga cikin manyan matakan kariya shi ne sanya wadanda suka ci gajiyar shirin yin rantsuwa da Alkur’ani kafin komawarsu cikin al’umma.
Ta ce yin rantsuwar shi ne mataki na karshe a tsarin gyaran hali na Borno, kuma yana dauke da manyan sakamakon addini ga mahalarta shirin.
Gambo ta ce:
“Idan suka zo gare mu bayan dukkan matakan tsarin Borno, abu na karshe shi ne suna yin rantsuwa da Alkur’ani. Duk wanda ya rantse da Alkur’ani ya san sakamakon hakan.”

Source: Original
Fargabar da gwamnati ta aka cire wa al'umma
Ta kara da cewa wasu mutane suna tunanin tsofaffin mayakan za su koma daji, amma idan suka yi hakan rayuwarsu za ta shiga hadari daga kungiyoyin ta’addanci.
A cewarta:
“Da zarar mutum ya fita daga daji ya mika wuya ga hukuma, ya zama kafiri a idanun kungiyar ta’addanci saboda haka zai shiga matsala.”
Kwamishiniyar ta bayyana rashin isasshen kudi a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da ke hana gudanar da shirin cikin sauki da inganci.
Ta ce gwamnati na fuskantar matsalar ciyarwa, tufatarwa da samar da ilimi ga mutane masu yawa da ake karbar su cikin shirin gyaran hali, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Borno
Muƙabala kan shirin gwamnatin tarayya mai suna Operation Safe Corridor ta kara zafi bayan kammala horas da tsofaffin mayakan Boko Haram 744 domin mayar da su cikin al’umma.
Daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, mutum 597 sun fito daga Borno, yayin da sauran suka fito daga Adamawa, Yobe, Kano da wasu wurare daban-daban.
Mutane da dama sun nuna damuwa kan yadda ake gudanar da shirin, musamman batun gaskiya, rikon amana da kuma kula da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Yadda ake horas da tubabbun Boko Haram
A wani labarin, an ji cewa hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa tsofaffin mayakan Boko Haram kimanin 800 na cikin shirin gyaran hali a Najeriya.
Tsofaffin 'yan ta'adda kusan 129,000 daga cikin 'yan Boko Haram da iyalansu sun mika wuya ga dakarun rundunar sojin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun bayyana cewa ana amfani da dabaru daban daban wajen ganin an kawar da 'yan Boko Haram da sauran miyagu.
Asali: Legit.ng
