Latest
Masu ababen hawa dake bin babbar hanyar titin jami’ar Bayero ta Kano sun shiga cikin zulumi yayin da hukuma ta rufe hannu daya na titin sakamakon tsagewa da babbar gadar kasa ta Gadon Kaya ta yi
A yanzu haka, wani sashen ma'aikatar hukumar bada agaji na gaggawa ta kasa wato NEMA dake Abuja na ci bal-bal. Hakazalika an bankawa motocin hukumar biyu wuta kuma jami'an kwana-kwana na cikin kashe wutan yanzu
Yayinda yan Najeriya ke alhinin mutuwar Misis Obianuju Ndubusi-Chukwu, wata shugabar inshora ‘yar Najeriya wacce aka kashe a kasar Afrika ta kudu, kasar ta kuma fadawa cikin wani yanayi sakamakon kisan wani matashi da aka sake yi
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa, a safiyar ranar Lahadi, 21 ga watan Yuli, fitattun furodusoshin masaa’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood guda biyu, Usman Mu’azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hatsarin mota.
Wassu yan bindiga wadanda ba a san asalinsu ba sun yi garkuwa da wasu matafiya mata uku da ke a hanyarsu ta zuwa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa daga jihar Lagas.
Da yake dai a koda yaushe na gari ba sa karewa duk da dai a wannan zamani sai an tona, mun samu cewa wani karamin ma'aikacin sojan sama na Najeriya, Bashir Umar, ya yi tsintuwar dukiya mai tarin yawa kuma ya mayar wa da mai ita.
A yanzu haka ana iya cewa zaman lafiya ya fara samuwa a jahar Zamfara sakamakon sulhu da gwamnan jahar, Bello Matawalle ya fara yi da yan bindiga, inda a yanzu haka sun sake sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu.
Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Anambra ta bayyana yadda wani katon bera ya lallabo ya yanke tare da cinye kunnen wani jariri sabon haihuwa a Asibitin Victory dake garin Onitsha na jahar Anambra.
Hukumomi a kasar Indiya sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon wata tsawa da aka yi a jihar arewacin Indiya da ke Uttar Pradesh.
Masu zafi
Samu kari