Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu

Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta kudu

Yayinda yan Najeriya ke alhinin mutuwar Misis Obianuju Ndubusi-Chukwu, wata shugabar inshora ‘yar Najeriya wacce aka kashe a kasar Afrika ta kudu, kasar ta kuma fadawa cikin wani yanayi sakamakon kisan wani matashi da aka sake yi a kasar.

Ndubisi-Chukwu ta kasance mataimakiyar Darakta-Janar na cibiyar Injora na Najerya (CIIN) sannan kuma an kasha

An harbi Chinonso Dannis Obiaju, dan shekara 17 wanda ya kasance dalibi a Johannesburg a ranar Asabar.

Shugaban kungiyar yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, Mista Adetola Olubajo, wanda ya tabbatar da kisan ga manema labarai, yace marigayin na zama ne a Roodeprt, Johannesburg tare da mai kula dashi.

Olubajo said on telephone that the late boy’s guardian, Mr Mike Nsofor, disclosed that he was shot at about 6.30 p.m.

Olubajo ya bayyana a wayar tarho cewa mai kula da yaron, Mista Mike Nsofor, ya bayyana cewa an harbi yaron ne da misalin karfe 6:30 na yamma.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Furodusa Usman Mu'azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hatsarin mota

“Ya je siyan abu a wani shago tare da abokinsa sannan wani ya fara binsu yana bude masu wuta, inda ya kashe shi,” inji mai kula dashi.

Ya kara da cewa iyalan za su binne shi a Afrika ta kudu, inda yace shugabannin kungiyar a Johannesburg za su dunga tuntubar shi don jin yadda ake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel