Gwamna Ya Tube Rawanin Sarkin da aka Samu da Laifin Damfara a Amurka
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ya dauki matakin tube rawanin daya daga cikin sarakunan da ke jihar
- Ademola Adeleke ya amince da tube rawanin Apetumodu na Ipetumodu, Oba Joseph Oyedele, bayan an same shi da laifi
- Basaraken dai an yanke masa hukunci a kasar Amurka bayan wata kotu ta same shi laifin da ya danganci damfara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya amince da tube rawanin Oba Joseph Oloyede daga matsayin Apetumodu na Ipetumodu.
Wannan shawara ta biyo bayan samun Oloyede da laifi da aka yi a ƙasar Amurka kan zargin damfara ta haraji da kuma halasta kuɗaɗen haram.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa wadda kakakin gwamnan, Olawale Rasheed, ya fitar a shafin X gwamnatin jihar Osun a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.
Matakin gwamnan ya zo ne bayan samun tabbataccen kwafi na hukuncin kotun Ohio, wadda ta yanke wa sarkin hukunci.
Sanarwar ta tunatar da cewa majalisar zartarwa ta jiha ta yanke shawara a shekarar da ta gabata cewa ma'aikatar kananan huumomi ta rubuta wa kotun Ohio wasiƙa domin neman tabbataccen kwafi na hukuncin don ya zama tushen matakin da gwamnati za ta dauka.
"Majalisar zartarwar ta ba da hujjar shawarar tuntuɓar kotun Ohio a kan cewa bai kamata a gina shawarwarin gwamnati a kan rahotannin kafofin sada zumunta kaɗai ba."
“A cikin takardar tsigewar da Mai girma gwamna ya sanya wa hannu a ranar 7 ga Mayu, 2026, an gina matakin ne a kan buƙatar kiyaye zaman lafiya, doka da oda, da kyakkyawan shugabanci, da kuma kiyaye daraja da mutuncin gidan sarautar."
“Takardar tsigewar ta ƙara bayyana cewa halayyar damfara ta Oba Joseph Oloyede, kamar yadda kotun Amurka ta tabbatar kuma ya amsa laifinsa, da kuma shari’arsa a idon duniya da hukuncin da aka yanke masa."
"Sun zubar da mutuncin masarautar da Apetumodu na Ipetumodu tare da sanya su cikin abin kunya a idon jama’a, wanda hakan ya sa aka koma ga matakin tsigewa.”
"Sakamakon wannan tsigewa, kujerar Apetumodu na Ipetumodu ta zama fanko, yayin da za a samar da hanyoyin da suka dace don naɗa sabon Apetumodu na Ipetumodu a lokacin da ya dace.”
“Gwamnan yana kira ga ’ya’ya maza da mata na Ipetumodu da su kasance masu zaman lafiya da bin doka yayin da ake gudanar da tsarin naɗa sabon sarki.”
- Olawale Rasheed
An cafke basarake a Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar FBI ta Amurka ta cafke sarkin masarautar Ipetumodu, da ke jihar Osun, Kudu maso Yammacin Najeriya, Oba Joseph Oloyede.
An kama Oba Joseph Oloyede bisa zarginsa da hannu a satar kudaden tallafin COVID-19 wadanda suka kai kusan dala miliyan 4.2.
Takardun shigar da kara na kotun Amurka sun bayyana cewa an kama Oloyede a ranar 4 ga Mayun 2024, bayan samun takarardar izinin kama shi.
Asali: Legit.ng

