Mombasa: Dangote Ya Samu Birni a Afrika, Zai Gina Sabuwar Matatar Mai Ta $17bn

Mombasa: Dangote Ya Samu Birni a Afrika, Zai Gina Sabuwar Matatar Mai Ta $17bn

  • Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana birnin Mombasa na kasar Kenya a matsayin inda ya fi sha’awar gina sabuwar matatar mai
  • Aikin wanda zai lakume dala biliyan 17, zai tace danyen mai daga Uganda da sauran sassan duniya don amfanin Gabashin Afirka
  • Akwai takaddamar diplomasiyya tsakanin Kenya da Tanzania game da inda ya kamata Dangote ya gina wannan katafariyar matatar

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kenya - Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa yana nazarin canza tunanin gina matatar mai daga kasar Tanzania zuwa Kenya.

Alhaji Aliko Dangote, wanda ya kaddamar da matatarsa ta Legas a shekarun baya, ya ce yana da burin gina katafariyar matatar, mai iya tace ganga 650,000 a birnin Mombasa na kasar Kenya.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Alhaji Aliko Dangote ya shirya gina katafariyar matatar man fetur a Kenya.
Alhaji Aliko Dangote, attajirin Afrika da ke shirin gina matatar mai a Kenya. Hoto: Tom Saater/Bloomberg via Getty Images
Source: Getty Images

Dangote zai gina matatar mai a Kenya

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Financial Times, Dangote ya nuna cewa yanayin tashar jirgin ruwan Mombasa da girman tattalin arzikin Kenya sun fi ba shi kwarin gwiwar zuba wannan babban jari.

Yayin da yake fadin dalilan da suka sa ya fi samun nutsuwar gina matatar a Kenya fiye da birnin Tanga na Tanzania, Dangote ya ce:

“Ina sha’awar gina matatar man a Mombasa ne saboda tana da tashar jirgin ruwa mai zurfi da faɗi sosai. 'Yan Kenya sun fi samun ci gaban abubuwa, kuma tattalin arzikin kasar ya fi girma.”

Wannan shiri na gina matatar da za ta ci tsakanin dala biliyan 15 zuwa biliyan 17, na zuwa ne daidai lokacin da katafariyar matatarsa ta Legas ta ke aiki gadan-gadan a matsayin matatar mai mafi girma a duniya da ke amfani da na'ura daya.

Kara karanta wannan

Dan damfara ya sace wa mahajjaciya 'yar Najeriya daloli a Madina

Tasirin siyasa da diflomasiyya a gabashin Afirka

Wannan aiki, wanda ake sa ran zai tace danyen mai daga kasar Uganda, ya riga ya fara haifar da rarraba kawuna da takaddamar diflomasiyya tsakanin shugabannin yankin.

Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta nuna rashin jin dadinta bayan da takwararta na Kenya, William Ruto, ya yi sanarwa kan aikin ba tare da tuntubarta ba.

Dangote ya jaddada cewa nasarar wannan babban kuduri ya dogara ne kacokan kan goyon bayan gwamnati, inda ya bayyana cewa:

“Shugaba Ruto ne mai wuka da nama. Duk abin da shugaba Ruto ya ce, shi ne zan yi.”
An ce Danote na son gina matatar Kenya don tace danyen mai daga Uganda da sauran sassan duniya don amfanin Gabashin Afirka.
Matatar man fetur ta Dangote da ke Legas da hoton Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Bloomberg/Getty Images
Source: UGC

Dangote yana mutunta zabin Tanzania

A cewar Dangote, danyen man da matatar za ta rika amfani da shi za a iya jigilar sa ta cikin jiragen ruwa, saboda haka ba lallai sai an gina matatar kusa da bututun man da ya tashi daga Uganda zuwa gabar tekun Tanzania ba.

Duk da fifikon da ya ba wa Kenya, attajirin ya bayyana cewa har yanzu Tanzania tana da dama idan har za su iya sasanta takaddamar da ta dabaibaye shawarar aikin a kasar tasu, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Wannan mataki na Dangote dai ana kallon sa a matsayin wata dabarar neman yarjejeniya mafi kyau daga kasashen biyu kafin ya zabi wacce zai yi aiki a cikin ta.

Dangote zai shiga harkar wutar lantarki

A wani labari, mun ruwaito cewa, attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya shiga zuba jari mai girma a fannin samar da wutar lantark.

Dangote, wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka ya ce kamfaninsa zai samar da wutar da ta kai megawatt 20,000.

A halin yanzu, Najeriya na samar da kusan megawatt 4,000 zuwa 4,500 na wutar lantarki, adadin da ya yi ƙasa sosai da adadin da ake bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com