Iran tace ta kama yan leken asirin Amurka guda 17, ta yanke ma wasu hukuncin kisa

Iran tace ta kama yan leken asirin Amurka guda 17, ta yanke ma wasu hukuncin kisa

-Kasar Iran ta kama yan leken asiri su 17 wanda suke jami’an kasar Amurka kuma an yanke ma wasu hukuncin kisa.

-Wani ma’aikacin hukumar samun bayanan sirri na kasar Iran wanda ya bukaci aboye sunan shi yace jami’an tsaro sun samu nasarar kamo yan leken asirin da rushe gungun jami'an kamar yadda ya bayyana ma manema labarai a Tehran a yau litinin.

Kasar Iran ta kama yan leken asiri su 17 wanda suke jami’an kasar Amurka kuma an yanke ma wasu daga ciki hukuncin kisa.

Wani ma’aikacin hukumar samun bayanan sirri na kasar Iran wanda ya bukaci aboye sunan shi yace jami’an tsaro sun samu nasarar kamo yan leken asirin da rushe gungun jami'an kamar yadda ya bayyana ma manema labarai a Tehran a yau litinin.

“Wadan da suka ci amanar kasa da gan-gan an kai su kotu.” Ya ce wasu an yanke masu hukuncin kisa wasu kuma zasu zauna gidan kaso na lokaci mai tsawo.

Wannan bayanan na zuwa ne bayan zaman dar-dar da kasar Iran da ta Amurka wanda ya faro bayan shawarar gwamnatin Amurka na ficewa daga yarjejeniyar nuclear a 2015 da kuma kakaba wa Iran takunkumin tattalin arziki.

KARANTA WANNAN: Kudin alawus N8.5m, da ake bamu a wata ya yi kadan - Dan majalisan wakilai

Ya kuma ce cikin mutanen 17 babu wanda yayi cijiya a samemen da aka kai masu.

Takamaiman aikin su shine samun bayanai a ma’aikatun da suke aiki tare sanya na’ura mai kula da aikace-aikace, da kuma aike da sakon bayanan.

Wasu cikin su masu sha’awar samun takarda tafiya Amurka ne, da wannan ne jami'an suka jasu cikin aikin. “ jami'an suna samun masu neman takardun tafiya ko kuma wanda takardun su ke da bukatar sabuntawa.”

Wani tarihi da aka nuna a gidan talabijin ranar litinin ya nuna wani jami’in yana koyawa wani dan kasar iran a hadaddiyar daular larabawa .

Sai dai kawo yanzu Amurka ba tace komai ba

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel