Wurare 5 da Mata ke auren fiye da namiji daya a lokaci guda

Wurare 5 da Mata ke auren fiye da namiji daya a lokaci guda

A yayin da auren fiye da mace daya ga mazaje ya samu karbuwa tare da kasancewarsa al'ada a tsakanin kabilu daban-daban a fadin duniya, a wasu wuraren duk da kasancewar su kalilan, wannan lamari ya kan tabbata amma a baibai.

Wasu kabilu a fadin duniya sun yarjewa Mata auren fiye da Miji daya a lokaci guda inda a wani sa'ilin wasun su sun yi na'am ga 'yan uwan juna biyu da suka fito daga tsatson iyaye daya su kasance Mazajen Mace guda.

Banbancin al'adu a fadin duniya ya sanya wasu kabilu suka yarjewa Miji ya sauka daga gadon sa na aure domin bai wa wasu mazajen damar kwanciya da Matar sa musamman baki wanda a cewar su hakan wani babban nau'i ne karamci da kuma kara.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku jerin wasu kasashe biyar da wannan al'ada ta baibai ta tabbata inda a wasun kuma take ci gaba da ta tabbata:

1. Najeriya

Kabilar Irigwe dake Yammacin jihar Filato.

Tsawon shekaru aru-aru, al'ummar wannan yankin sun yarjewa Mata auren miji fiye da daya inda suka da damar tsallakawa daga kan wannan miji zuwa wannan miji kuma idan ta raya masu su koma wurin wanda suka ga dama bisa ga ra'ayi. Sai dai an yi watsi da wannan bakar al'ada a shekarar 1968.

2. Kenya

Kabilar Maasai masu alkarya a Arewa, Tsakiya da kuma Kudancin kasar Kenya gami da wani bangare na Arewa kasar Tanzania. Sai dai an yi watsi da wannan al'ada ta bai wa Mata damar auren fiye da namiji daya.

3. India

A na yin wannan mummunar al'ada ta auratayya a yankin Jaunsar-Bawar a garin Uttarakhand. Wasu mutane da ake kira Paharis dake rayuwa a yankin Himalayas a Arewacin kasar India da kuma Kudu maso Gabashin Kashmir zuwa wasu yankuna na Nepal. Sai dai wannan al'ada ta fi tsanani a yankin Kinnaur, wani yanki na Himachal a kasar Indiya daf da gabar kasar Indonesia.

KARANTA KUMA: 'Yan daban daji sun kai hari jihar Katsina

4. China

Al'adar bai wa Mata damar yawace-yawace a tsakanin Maza ta tabbata cikin kabilar Tibet, wani yankin na Nepal dake kasar Sin har zuwa shekarar 1960.

5. Brazil

Kabilar Bororo na kasar Brazil dake rayuwa a jihar Mato Grosso. Hakazalika kabilar Tupi mazauna Kudu maso Gabashin kasar Brazil sun yi wannan al'ada tsawon shekaru 2,900 da suka gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel