Manyan Mata 9 na Najeriya da suka samu nasarar rayuwa

Manyan Mata 9 na Najeriya da suka samu nasarar rayuwa

Akwai wasu fitattun mata a Najeriya da suka nuna kwazo da kuma bajintar su a fannin harkokin kasuwanci da jagoranci. Kasar Najeriya ta tara manyan mata da suka kasance hamshakan 'yan kasuwa.

Da yawa daga cikin su sun kai kololuwa ta fuskar nasara a fagen sana'o'in su a sakamakon jajircewa, juriya, da kudirta kyakkyawar aniya da yiwa kawunan su fata na gari.

A yayin da ake yiwa kudi kirari da masu gidan rana, hakan ta kasance ga wannan hamashakan mata da suka tara dukiya mai dumbin yawa. Hakan ya sanya suka zamto mashahurai tare da yin tasiri mai girman gaske a tsakanin al'umma.

Jaridar Legit.ng ta kawo jerin sunayen wannan manyan mata, sana'o'i da kuma shekarun su na haihuwa kamar haka:

1. Stella Chinyelu Okoli

Shekarun haihuwa: 75

Mai kamfanin magunguna na Emzor Phamaceuticals

2. Folorunsho Alakija

Folorunsho Alakija
Folorunsho Alakija
Asali: UGC

Shekarun haihuwa: 68

Ta kasance dayya daga cikin hamshakan attajirai na duniya a sakamakon harkokin kasuwanci na man fetur da ma'adanansa.

3. Mo Abudu

Mo Abudu tare da mijin ta
Mo Abudu tare da mijin ta
Asali: Instagram

Shekarun haihuwa: 54

Mai kamfanin talabijin na Ebony TV. Ta shahara a kan sana'ar nishadantar wa.

4. Oby Ezekwesili

Oby Ezekwesili
Oby Ezekwesili
Asali: UGC

Shekarun haihuwa: 56

Tsohuwar ministan ilimi a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ta kasance mataimakiyar shugaban bankin duniya a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012. Masaniyar tattalin arzikin ta mallaki kamfanin Bharti Airtel.

5. Biola Alabi

Shekarun haihuwa: 50

Ta mallaki kamfanin sadarwa da nishadantarwa na Biola Alabi Media.

6. Betty Irabor

Betty Irabor
Betty Irabor
Asali: Instagram

Shekarun haihuwa: 62

Ta shahara a harkokin nishadantarwa kuma ta mallaki kamfanin sadarwa wajen wayar da kai gami da mallakar mujallar Genevieve Magazine.

7. Linda Ikeji

Linda Ikeji
Linda Ikeji
Asali: UGC

Shekarun haihuwa: 38

Ta mallaki kamfanin sadarwa na Linda Ikeji Media

8. Tara Fela-Durotaye

Tara tare da mijin ta Fela-Durotaye
Tara tare da mijin ta Fela-Durotaye
Asali: Instagram

Shekarun haihuwa: 42

Ta yi kaurin suna a kan sana'ar yiwa mata kwalliya. Ta mallaki kamfanin kwalliyar mata mai sunan House of Tara.

9. Funmi Iyanda

Shekarun haihuwa: 47

Funmi ta yi fice a kan sana'ar sadarwa. Ta mallaki kamfanin talabijin na Creation Television UK

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel