Mahajjatan Najeriya 16, 605 su na kasar Saudi da nufin aikin Hajji

Mahajjatan Najeriya 16, 605 su na kasar Saudi da nufin aikin Hajji

Mutanen Najeriya fiye da 16, 000 su na kasa mai tsarki domin aikin Hajjin bana kamar yadda mu ka samu labari. Jaridun cikin gida sun nuna cewa jirage kusan 34 ne su ka bar Najeriya yanzu.

Kawo yanzu Maniyyata 16, 605 daga Najeriya su ka bar gida zuwa Garin Makkah da Madina a kasar Saudi Arabia. Hakan na zuwa ne bayan jirgin yau, 22 ga Watan Yulin 2019, ya tashi.

Jirgin yau din Litinin ya tashi ne daga jihar Sokoto zuwa Birnin Madina da kimanin karfe 06:55. Rahotanni sun bayyana cewa wannan jirgi ya na dauke da Maniyyata maza da mata guda 429.

Maniyyatan sun tashi ne daga jihohin Oyo, Osun, Ogun, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, Nasarawa, Kebbi, Kwara, Kogi, Sokoto, Zamfara da kuma jihar Legas da babban birnin tarayya.

KU KARANTA: Alaranmomi 20, 000 za su shiga babban Gasar Musabaqa a Saudi

A halin yanzu Maniyyatan kasar musamman wadanda su ka fito daga Legas sun bar Garin Madinah zuwa Makkah inda za su yi Umrah. Za su yi umran ne kafin lokacin da za a sauke farali.

Babban Limamin ‘yan sandan Najeriya. Dr Alhassan Yaqub, ya shawarci ‘yan Najeriya da su rika kai ziyara zuwa Birnin Manzo watau Madinah inda kabarin Annabi Muhammad SAW ya ke.

Musulunci ya kwadaitar da tarin lada mai yawa ga wanda ya yi sallah a masallacin harami na Makkah da na Madina. Masallacin Quba da dutsen Uhudu su na cikin wurare masu daraja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng