Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Tsawa ta kashe mutane 33

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Tsawa ta kashe mutane 33

Hukumomi a kasar Indiya sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon wata tsawa da aka yi a jihar arewwacin Indiya da ke Uttar Pradesh.

Jami’in hukumar bayar da agaji na kasar Sandhya ya bayyana cewa tsawar wacce ta sauka a ranar Lahadi ta kashe mutane 33 sannan ta raunata wasu 13.

Jami’in ya kuma bayyana cewa gidaje 20 ne suka rufsa sakamakon tsawar.

Ruwa mai karfi da tsawa sun barke a yankin lokacin da manoma ke aiki a gonakinsu.

Wani jami’in sashin kimiyar yanayi na Indiya, J.P. Gupta ya bayyana cewa dan samu matsin lamba ne ta bangaren iskar da ta kado.

Jami’in dan sanda Pradyuman Singh ya bayyana cewa mutane bakwai sun mutu a kauye guda yayinda suke aiki a gona, ciki harda wata mata da dan karamin yaro.

KU KARANTA KUMA: Abunda muke so gwamnati tayi mana – Kungiyar Makiyaya

Uttar Pradesh babban ministan Yogi Adityanath yace za a ba iyalan wadanda suka mutu diyar kimanin dala 6,000.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani mutumi mai sune Tijjani Yahaya mai shekara 57 a duniya, kan zargin kashe kaninsa mai suna Aminu mai shekara 20 ta hanyar caka masa wuka.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da afkuwar al’amari inda ya bayyana cewa Aminu ya cika ne a asibiti kwararru na Murtala Mohammed, yayinda ake kokarin ceto ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng