Yanzu-yanzu: Yan Shi'a sun hallaka babban jami'in dan sanda, DCP Usman Umar

Yanzu-yanzu: Yan Shi'a sun hallaka babban jami'in dan sanda, DCP Usman Umar

Mataimakin kwamishanan yan sanda mai kula da ayyukan hukumar a birnin tarayya Abuja ya rigamu gidan gaskiya.

DCP Usman Umar, ya rasu ne a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli sakamakon rikicin da ya barke tsakanin yan Shi'a da jami'an yan sanda a cikin garin Abuja.

Mutuwarshi ya tayar da hankali gidan yan sanda inda abokan aikinsa suka siffanta wannan abu a matsayin abin takaici.

Umar, ya kasance babban na kusa da tsohon sifeton yan sanda, Ibrahim Idris, kafin aka nadashi shugaban ayyukan hukumar na Abuja.

KU KARANTA: Kotun zabe tayi watsi da karar da ke kalubalatar nasarar Gwamna Bagudu

Rahoton ya bayyana cewa yan Shi'an sun harbe jami'in dan sanda ne yayinda yake kokarin hanasu tare hanyar tafiyan motoci da yan kasuwa a cikin birnin tarayya a yau.

Da wuri aka garzaya da shi asibiti inda ya kwanta dama.

Yan kungiyar Shi'a mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky da suke gudanar da zanga-zanga suka bankawa ma'aikatar wuta lokacin da yan sanda suka hanasu zanga-zanga.

Zanga-zangar wacce suka fara daga tashan NITEL Junction dake Wuse 2 ya samu cikas ne yayinda yan sanda suka toshe hanyar zuwa majalisar dokokin tarayya da fadar shugaba kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel