Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya 3, sun bukaci a basu N30m

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya 3, sun bukaci a basu N30m

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya mata uku da ke a hanyarsu ta zuwa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa daga jihar Lagas. Wadanda aka sace sun hada da Okuboere, Seifefa da Amara.

An tattaro cewa ana zargin makiyaya ne suka sace su a yankin Okada da ke jihar Edo.

Princess Grace wacce ta kasance mazauniyar Bayelsa, ta bayyana wadanda lamarin ya cika dasu a matsayin surukanta da kuma abokiyarsu daga jihar Abia, Amara.

Grace tace lamarin ya auku ne da misalin karfe 12:00 na ranar Lahadi, inda ta kara da cewa yan bindigan sun nemi a basu kudin fansa naira miliyan 30 domin su sako su.

Tace: “Wasu da ake zargin makiyaya ne a hanyar Okada Road da ke jihar Edo sun yi garkuwa da surukaina, Okuboere, Seiyefa da kawarsu Amara daga jihar Abia, da misalin karfe 12:00 na rana.

“Sun kasance a hanyarsu na zuwa Yenagoa daga jihar Lagas tare da yara biyu a motan.

“An kawo cewa yan ta’addan sun harbe su ta gaba sannan yayinda suka yi kokarin juyawa, sai suka far masu ta baya.

“Sun fito daga karamar hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa yayinda kawarsu ta fito daga yankin Arochukwu da ke jihar Abia.

KU KARANTA KUMA: Abunda muke so gwamnati tayi mana – Kungiyar Makiyaya

“An bar yaran da suka kasance yan shekara 12 da 4 a cikin mota a dajin da lamarin ya faru.

“A daren jiya, daya daga cikin wadanda aka sa ceta kira ni don na sanar ma iyayensu cewa masu garkuwan na neman a basu naira miliyan 30. An sanar ma da yan sandan jihar Edo.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng