Kannywood: Furodusa Usman Mu'azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hatsarin mota

Kannywood: Furodusa Usman Mu'azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hatsarin mota

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa, a safiyar ranar Lahadi, 21 ga watan Yuli, fitattun furodusoshin masaa’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood guda biyu, Usman Mu’azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hatsarin mota.

Sun yi hatsarin ne a daidai garin Dakatsalle da ke jihar Kano yayinda suke a hanyarsu ta zuwa babbar birnin tarayya, Abuja.

An tattaro cewa a dayar motar da hatsarin ya cika dasu mutane uku ne suka rasa rayukansu, sai dai kuma babu wanda ya mutu a cikin motar furodusoshin na Kannywood, amma dai an samu rauni.

Bayan nan an dauki su Usman zuwa asibitin Malam Aminu Kano, inda aka gano cewa Usman Mu’azu ya bugu a kirji.

Kannywood: Furodusa Usman Mu'azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hadarin mota
Kannywood: Furodusa Usman Mu'azu da Abba Miko Yakasai sun yi mummunan hadarin mota
Asali: Twitter

A halin da ake ciki an sallame shi, inda yanzu haka yana gida yana jinya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya 3, sun bukaci a basu N30m

A wani lamari na daban, Legit.ng ta kawo cewa hukumomi a kasar Indiya sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon wata tsawa da aka yi a jihar arewwacin Indiya da ke Uttar Pradesh.

Jami’in hukumar bayar da agaji na kasar Sandhya ya bayyana cewa tsawar wacce ta sauka a ranar Lahadi ta kashe mutane 33 sannan ta raunata wasu 13.

Jami’in ya kuma bayyana cewa gidaje 20 ne suka rufsa sakamakon tsawar. Ruwa mai karfi da tsawa sun barke a yankin lokacin da manoma ke aiki a gonakinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel