Ta Tabbata Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnonin APC, Uba Sani Ya Yi Bayanai

Ta Tabbata Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnonin APC, Uba Sani Ya Yi Bayanai

  • An samu rahotannin da ke nuna cewa an samu a cikin kungiyar gwamnonin da ke karkashin inuwar jam'iyyar APC
  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ba da tabbacin cewa an samu sabani a cikin kungiyar gwamnonin na APC
  • Ya bayyana cewa an warware matsalar da ta taso kuma ba a samu sauyin shugabanci ba a kungiyar wadda ke karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodimma

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan rikicin da aka samu a tsakanin gwamnonin jam'iyyar APC.

Gwamna Uba Sani ya ce rikicin da aka samu a kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) "ɗan rashin fahimta ne kawai."

Uba Sani ya yi magana kan rikici tsakanin gwamnonin APC
Gwamnonin jam'iyyar APC bayan sun kammala taro Hoto: @HopeUzodimma
Source: Twitter

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 11 ga watan Mayun a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan Arewa za su zabi Tinubu a 2027,' Uba Sani ya fito da bayanai

Rigima ta taso a kungiyar gwamnonin APC

A makon da ya gabata ne aka samu rahotannin cewa an tsige gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, daga shugabancin PGF tare da mayurbinsa da Peter Mbah, gwamnan jihar Enugu, bayan wani taro mai cike da takaddama da aka yi a Abuja.

Bayan haka, labarai sun yaɗu cewa ƙungiyar gwamnonin APC ta rarrabu zuwa gida biyu.

Uzodimma ya dage kan cewa shi ne har yanzu shugaban ƙungiyar, yayin da aka ce wani ɓangaren kuma yana marawa Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, da Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan jihar Kwara baya.

Sai dai, daga baya gwamnonin da ke goyon bayan Uzodimma sun nuna gamsuwarsu da shugabancinsa yayin wani taro da suka yi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Abuja.

Me Gwamna Uba Sani ya ce kan rikicin?

Gwamna Uba Sani, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar, ya ce yanzu an warware saɓanin da ke tsakanin gwamnonin.

“A ra’ayi na, ba na jin wannan wata babbar matsala ce, kamar yadda mutane da yawa ke ƙoƙarin nuna ta a matsayin wani babban al’amari."

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 sun kawo uzuri, ba su halarci tantancewar APC gabanin zaben 2027 ba

“Domin kuwa, ku sani, duk abin da muke magana akai dimokuradiyya ce, mutane za su iya zaɓar rashin amincewa da juna sannan daga baya su amince. Saboda haka, a gani na, ɗan rashin fahimta ne kawai.”
“A halin yanzu babu wata matsala. Dukkan gwamnoni suna tare. Mai girma Hope Uzodimma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC. Ni kaina, Sanata Uba Sani, ni ne mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin APC.”

- Gwamna Uba Sani

Babu sauyin shugabanci a kungiyar PGF

Gwamnan na Kaduna ya kuma ce ba a yi wani canjin shugabanci a ƙungiyar ba.

“Ba na jin za ku sake jin komai. Ina ba ku tabbacin cewa, babu abin da zai sake faruwa, ba za ku sake jin komai ba."

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya yi magana kan rikicin gwamnonin APC
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Me ya haddasa rikici a kungiyar PGF

Yayin da aka tambaye shi game da saɓanin da aka samu a ƙungiyar, Gwamna Uba Sani ya ce rashin jituwa tsakanin ’yan siyasa ba baƙon abu ba ne.

“Yana da kyau a samu saɓani. Amma kamar yadda na faɗa, magana ta a sarari take. Ba za ku taɓa jin komai ba."
“Wani ɗan saɓani ne kawai, ba wata babbar matsala ba ce, amma ɗan saɓani ne. Kuma an riga an warware shi.”

Kara karanta wannan

APC ta tara N4.4bn daga sayar da fam na takarar 2027 duk da rikicin jam'iyya

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya magantu kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Uba Sani ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa ’yan Najeriya, musamman 'yan Arewa, za su zaɓi shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu a zaben 2027.

Gwamnan na Kaduna ya kalubalanci ’yan adawa, waɗanda ke yawan sukar shugaban ƙasa, a kan sauyin da za su iya kawowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng