Lamari Ya Baci: Hisbah Ta Cafke Malamin Addini a Zamfara kan Zargin Neman Maza

Lamari Ya Baci: Hisbah Ta Cafke Malamin Addini a Zamfara kan Zargin Neman Maza

  • Dubun wani malamin addini da ake zargi da neman maza ta cika a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Hukumar Hisbah ta bayyana cewa ta yi caraf da malamin addinin wanda ake zargi da tura hotunan tsiraicinsa ga wani matashi
  • Hisbah ta bayyana cewa malamin addinin ya amsa laifinsa inda ya bayyana cewa ya dade yana tare da wannan mummunar dabi'ar

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Gusau, jihar Zamfara - Hukumar Hisbah ta jihar Zamfara ta samu nasarar damke wani malamin addini.

Hukumar Hisbah ta cafke malamin addinin ne kan zargin neman maza da kuma turawa wani saurayi hotunan tsiraicinsa da bidiyon masu neman maza ta wayar salula.

Hisbah ta cafke malamin addini a Zamfara
Shugaban hukumar Hisbha na Zamfara, Sheikh Umar Hassan Gusau Hoto: Umar Haruna Tsafe
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Hisbah ta jihar Zamfara, Malam Umar Haruna Tsafe, ya fitar a shafin Facebook a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tube rawanin sarkin da aka samu da laifin damfara a Amurka

Meyasa Hisbah ta cafke malamin addinin?

Sanarwar wadda jami'in hulda da jama'ar na hukumar Hisbah ya fitar, ta bayyana cewa an cafke malamin addinin ne a birnin Gusau bayan binciken da aka gudanar kan zargin da ake yi masa.

Rahoton ya ce hukumar Hisbah ta bayyana cewa yayin binciken da ta gudanar, malamin addinin ya amsa zargin da ake tuhumarsa da shi.

Malamin addinin ya sanar da hukumar Hisbah cewa ya dade yana aikata irin wannan hali tun lokacin da ya ke karatu a makarantar sakandire da ke GTC Maru.

Hisbah ta yi wa malamin addinin nasiha

Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Zamfara, Sheikh Umar Hassan Gusau, ya yi wa malamin nasiha mai ratsa jiki kan illar abin da yake aikatawa.

Hakazalika, Sheikh Umar Hassan Gusau, ya bayyana cewa bayyana masa sakamakon da addinin Musulunci ya tanada ga mutanen da ke aikata irin wannan laifi.

Shugaban na Hisbah ya kara da cewa a matsayinsa na malamin addini kuma shugaban makarantar Islamiyya, ba zai ci gaba da jagorantar ta ba saboda ka da ya gurbata tarbiyyar dalibai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa tarihi, ya kirkiri sabon ofishi a fadar shugaban kasa kan tsaro

Hisbah ta yi caraf da malamin addini a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wane mataki aka dauka kan malamin addinin?

Daga bisani, hukumar Hisbah ta dauki matakin mika malamin addinin ga kotun shari’ar Musulunci domin ci gaba da gudanar da bincike da daukar matakin da ya dace a kansa.

Daga karshe, hukumar Hisbah ta sanar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da daukar matakai kan duk mutumin ake zargi da aikata laifuffukan da suka ci karo da koyarwar addini da ka’idojin zamantakewa a jihar.

Hisbah ta cafke ango da amarya a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa biyar bisa zargin shirya aure ba bisa ka’ida ba, sannan tare da samun amincewar iyayen amarya ba.

Rahotanni sun nuna cewa an kulla auren ne da sadakin da ya yi kasa da kima, abin da ya sabawa tsarin Musulunci da doka.

Daga cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango da wasu mutum uku da suka shiga cikin shirin a matsayin shaidu da wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng