Da Gaske Seyi Ya Ce ko Ubangiji ba zai Hana Tinubu Tazarce a 2027 ba?
- Kungiyar Ƙungiyar City Boy Movement mai goyon bayan shgaba Bola Tinubu ta yi magana kan zargin da aka yi wa Seyi Tinubu kan zaben 2027
- Wani sako da aka yada a kafafen sadarwa ya yi zargin cewa Seyi Tinubu ya ce Allah ba zai iya hana mahaifinsa yin shekara takwas a kan mulki
- A martanin da ta yi kan jita-jitar, kungiyar ta bayyana matsayar Seyi Tinubu game da mutunta addini da dukkan abubuwan da suka shafi Ubangiji
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ƙungiyar City Boy Movement ta ce Seyi Tinubu bai taɓa cewa ko Ubangiji ba zai iya hana mahaifinsa yin shekara takwas a matsayin shugaban ƙasa ba.
A kwanakin baya, aka rika yada cewa dan shugaban kasar ya nuna cewa babu makawa sai Mai girma Bola Tinubu Ahmed ya yi tazarce a zaben 2027.

Source: Facebook
Zargin da aka yi wa Seyi Tinubu
The Cable ta wallafa cewa a kwanakin baya wani mai suna Albab Abdullahi ya wallafa wani labari inda ya yi zargin cewa Seyi ya yi wata magana ta “saɓo” dangane da burin mahaifinsa a zaɓen 2027.
“Babu wani abu da zai iya hana mahaifina cika shekara takwas a mulki. Ko Ubangiji ma ba zai iya ba,”
In ji zargin da Albab Abdullahi ya danganta wa Seyi.
Sai dai mutumin bai bayyana lokacin ko wurin da ake zargin ɗan shugaban ƙasar ya yi wannan magana ba kuma Legit Hausa ta samu wani bidiyo ko wata hujja da za ta nuna cewa Seyi ya faɗi kalaman da ake danganta masa ba.
Da gaske Seyi ya fadi haka?
A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban sadarwa da hulda da jama’a na ƙungiyar City Boy, O’tega Ogra ya fitar ranar Litinin, ya ce ɗan shugaban ƙasar bai yi wannan magana ta “saɓo” ba.

Kara karanta wannan
RHA ta kafa hujjoji, ta ce Shugaba Tinubu ya cika alkawuran da ya daukar wa 'yan Arewa
A wani sako da kungiyar ta wallafa a X, Ogra ya ce:
“Karya ne da aka shirya domin ɓata sunansa, karkatar da ƙimarsa da kuma haddasa rikicin addini marar amfani a ƙasar.”
“Domin kauce wa shakku, Seyi Tinubu bai yi maganar da ake danganta masa ba. Bai taɓa yin irin wannan magana ba a kowane lokaci, a ko’ina, ta kowace hanya ko a kowane yanayi,”
“Danganta wannan magana da shi ƙarya ce tsagwaronta. An yi ta ne da muguwar manufa, an yaɗa ta cikin rashin tunani kuma tana da haɗari."
Sanarwar ta kara da cewa:
“Barista Seyi Tinubu mutum ne mai addini wanda ke da cikakken girmamawa ga Allah Maɗaukakin Sarki. Yana da cikakken imani cewa dukkan iko na Allah ne shi kaɗai, kuma babu wani mutum da zai samu ko ya riƙe ko ya yi amfani da iko sai da yardar Allah da rahamarsa.”

Source: Facebook
'Tinubu zai yi nasara' - Uba Sani
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Uba Sani ya yi magana kan zaben shugaban kasa da za a yi a 2027, inda ya ce Bola Tinubu zai yi nasara.
Uba Sani ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa shugaban kasar zai samu goyon bayan jama'a a Najeriya, musamman a Arewa.
Gwamnan ya kalubalanci 'yan adawa masu sukar Bola Tinubu da su bayyanawa 'yan Najeriya mafitar da suke da ita kan matsalolin kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

