Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara

Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara

A yanzu haka ana iya cewa zaman lafiya ya fara samuwa a jahar Zamfara sakamakon sulhu da gwamnan jahar, Bello Matawalle ya fara yi da yan bindiga, inda a yanzu haka sun sake sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu.

Idan za’a tuna, a baya, jahar Zamfara ta yi kaurin suna wajen matsalar tsaro, inda ake yawan samun hare haren yan bindiga, satar shanu, garkuwa da mutane, wanda hakan ya sanya rashin amince tsakanin Fulani da Hausawa, tare da janyo asarar rayuka da dimbin dukiya.

KU KARANTA: Kamfanin wutar lantarki za ta jefa al’ummar jahar Kano cikin duhu

Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara
Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara
Asali: Facebook

Sai dai sabon gwamnan jahar Zamfara, Gwamna Matawalle ya zo da sabon salo, inda ya ga dacewar gudanar da zaman tattaunawa na sulhu tsakanin yan bindigan da gwamnati, da kuma yan kato da gora, kuma zuwa yanzu hakan bada sakamako mai kyau.

A wani labarin kuma, manyan kwamandojin kungiyoyin yan bindiga da suka addabi al’ummar jahar Zamfara sun saduda, inda a yanzu haka sun yi alkawarin dakatar da kai hare hare a karamar hukumar Birnin Magaji da kewwaye.

Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara
Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara
Asali: Facebook

Yan bindigan sun dauki wannan alkawari ne bayan wani zaman sulhu da aka gudanar tsakaninsu da gwamnatin jahar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a jahar a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuli.

An gudanar da wannan zama ne a fadar Sarkin Birnin Magaji Alhaji Hussaini Maude-Dan’Ali, kuma ya samu halartar kwamishinan Yansandan jahar Usman Nagogo, mashawarcin gwamnan Zamfara a kan harkar tsaro, Abubakar Dauran, da shuwagabannin kungiyar Miyetti Allah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel