Wata sabuwa: Gafiya ta cinye kunnen wani jariri a Asibitin Najeriya

Wata sabuwa: Gafiya ta cinye kunnen wani jariri a Asibitin Najeriya

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Anambra ta bayyana yadda wani katon bera ya lallabo ya yanke tare da cinye kunnen wani jariri sabon haihuwa a Asibitin Victory dake garin Onitsha na jahar Anambra.

Rahoton jarida Sahara ta ruwaito Yansandan sun bayyana haka ne cikin wani rahoto da suka hada, inda suka ce hukumar asibitin da ma’aikatan asibitin basu da hannu cikin bacewar kunnen jariri, suka daura alhakin hakan a kan wani bera.

KU KARANAT: Kamfanin wutar lantarki za ta jefa al’ummar jahar Kano cikin duhu

Tun a shekarar 2015 wannan lamari ya auku, inda iyayen yaron suka zargi hukumar asibitin da ma’aikatan asibitin do yanke kunnen yaronsu domin yin amfani dashi wajen tsafe tsafe, wanda hakan yasa aka kama wasu daga cikin ma’aikatan asibitin.

Kwatsam sai ga wani sabon rahoto daga ofishin babban sufetan Yansanda yana bayyana yadda bera ya cinye kunnen jaririn: “Game da batun yanke kunnen wani jariri da Mista Solomon Igwe ya kai karar Dakta Oliver Umeh tare da ma’aikatan asibitin Victory zuwa babban sufetan Yansanda.

“Da misalin karfe 7:30 na ranar 30 ga watan Yuli ne Solomn Igwe ya dauki gawar dansa daga asibitin, amma bude gawar keda wuya sai ya ga babu kunne a jikinsa, wanda hakan yasa ya zargi ma’aikatan asibitin da yanke kunnen.”

Rahoton ya cigaba da cewa daga nan aka kama shugaban asibitin, inda kuma Yansanda suka kaddamar da gudanar da bincike, yayin da Solomon ya dage lallai sai kwararrun likitoci sun duba gawar dan nasa don gano abinda ya kasheshi.

Daga karshe bayan kwararru sun gudanar da bincike a kan yaron har sau biyu, sa’annan yansanda suka gano ragowar kunnen yaron, sai bincike ya tabbatar da cewa bera ne ya guntule kunnen jaririn, kuma shine sanadiyyar mutuwarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel