Abba Gida Gida ya gabatar da shaidu 241 a kan Ganduje

Abba Gida Gida ya gabatar da shaidu 241 a kan Ganduje

A ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, ne jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida), suka gabatar da shaidu 241 a gaban kotun sauraron korafin zaben gwamna da ke zamanta a unguwar Bompai a Kano.

PDP da Abba na kalubalantar nasarar da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, dan jam'iyyar APC, ya samu a zaben kujerar gwamnan jihar Kano.

A cikin wadanda PDP da Abba ke kara a gaban kotun bayan Ganduje, akwai jam'iyyar APC da hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC).

Da yake gabatar da shaidun wadanda ya ke karewa, Mista Adeboyega Owomolo (SAN), lauyan masu kara, ya ce suna fatan gabatar da wasu karin shaidun domin tabbatar wa da kotun cewa an yi musu magudi a zaben gwamna a jihar Kano.

Owomolo ya shaida wa kotun cewa daga cikin shaidar da suka gabatar akwai takardun sakamakon zabe na asali (EC8As da EC8Bs) daga kananan hukumomin Albasu, Bebeji, Danbatta, Garun Malam, Gwarzo, Karaye, Kura, Madobi, Nasarawa, Rano, Rogo, Sumaila, Tudun Wada da Warawa da sauransu.

DUBA WANNAN: Farfesan Najeriya ya fadi wanda dillalan mulki ke son ya gaji Buhari, ya ce yaudarar Tinubu ake yi

Sai dai lauyoyin da ke kare wadanda ake kara, Mista Offiong Offiong (SAN) da Ahmad Raji (SAN), sun kalubalanci shaidun da bangaren masu kara suka gabatar a gaban ktun.

Offiong ya shaida wa kotun cewa masu kara sun kawo buhunhuna cikin zauren kotu sabanin takardun sakamakon zabe.

Amma, babbar alkaliyar kotun, Jastis Halima Shamaki, ta yi watsi da korafin lauya Offiong tare da karbar shaidun kafin ta daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yuli.

Kimanin shaidu 785 ake saka ran cewa zasu bayyana a gaban kotun domin bayar da shaida a bangaren APC da PDP dangane da zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a watan Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel