Allah kare: An rufe babbar hanya a Kano biyo bayan tsagewar gadar kasa

Allah kare: An rufe babbar hanya a Kano biyo bayan tsagewar gadar kasa

Masu ababen hawa dake bin babbar hanyar titin jami’ar Bayero ta Kano sun shiga cikin zulumi yayin da hukuma ta rufe hannu daya na titin sakamakon tsagewa da babbar gadar kasa ta Gadon Kaya ta yi, inji rahoton Kano today.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an rufe hanyar data tashi daga Gadon Kaya zuwa kofar Famfo dake makwabtaka da jami’ar Bayero bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a Kano, wanda hakan yasa gadar ba zata biyu cikin kwanciyar hankali ba.

KU KARANTA: Yan bindiga sun sako mutane 143 da suka yi garkuwa dasu a jahar Zamfara

Allah kare: An rufe babbar hanya a Kano biyo bayan tsagewar gadar kasa
Allah kare: An rufe babbar hanya a Kano biyo bayan tsagewar gadar kasa
Asali: Twitter

Ita dai wannan gada da aka sanya ma suna Abubakar Audu an ginatane a kan kudi naira miliyan 700 a zamanin tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya baiwa kamfanin Rocad kwangilar gina ta.

Haka zalika majiyar ta bayyana cewa gadar ta tsage ta sama sosai, saboda girman tsagun tasa ake tunanin gadar ka iya faduwa a kowanne lokaci, Allah Ya kiyaye, shi yasa aka rufe hanyar domin gudanar da gyare gyare a kanta.

Ruwan sama da aka sha kamar da bakin kwarya a cikin garin Kano ta mamaye wurare da dama, daga ciki har da gadar kasa ta Panshekara, wanda gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta gina.

A wani labari kuma, aiki ya yi nisa a gina gadar sama mai hawa uku a shataletalen Dangi wanda ake ginashi a kan kudi naira biliyan 4.5.

Jahar Kano na daga cikin jahohin Arewa mafi yawan gadoji sakamakon yawan jama’a da kuma adadin ababen hawa wanda ke kawo cunkoso a birnin Kano, gadojin sun hada da gadar Gadon Kaya, gadar Kwankwasiyya, gadar Kabuga, gadar Muratala Muhammad, gadar kofar ruwa da kuma gadar Panshekara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel