Latest
Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da aikin tantancewa tare da yi ma bakin haure mazauna jahar Sakkwato rajista tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kammala aikin titin daya tashi daga Abuja zuwa birnin Algiers na kasar Algeria.
Dakarun rundunar Sojan saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen ragargazan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a wani samame da suka kai musu yayin da suka taru a sansanoninsu a yankin tafkin Chadi.
Rahotanni sun kawo cewa an kashe shugaban makarantar sakandare na gwamnati na Tsokundi, mai suna Yusuf Yaro a wani sabon hari da aka kai hanyar Wukari-Tsokundi da ke karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.
Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kano sun tabbatar da ceto wani karamin yaro dan asalin jahar Kano da wasu miyagun mutane yan kabilar Ibo suka sace shi a shekarar 2014 suka kai shi jahar Anambra.
Kamar yadda rahoto daga Daily Post ya bayyana, an kama Uchenna ne bayan da wata mata mai suna Ruth Abdullahi ta kai wa ‘yan sanda rahoton yadda ya damfareta wasu kudade da mota kirar Toyota Camry mai lamba GU 514 LV.
Mukaddashin rijistaran makarantar, Uwargida Rebecca, wacce ta saka hannu a kan takardun korar ma'aikatan, ta ce sallamar ma'aikatan biyayya ce ga umarnin kwamitin da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nada a kan makarantar
Wani Abokin Mamman Daura ya musanya tulin sharrin da ake yi masainda ya bayyana gaskiyar rade-radin karfin ikonsa a mulkin Buhari ashe cewa Minista guda rak ya taba samu.
Yayan majalisar dokokin jahar Gombe sun yi awon gaba da mataimakin kaakakin majalisar, Shuaibu Haruna dake wakiltar mazabar Kwami ta gabas ta jahar biyo bayan kada kuri’un rashin gamsuwa da shi da suka yi.
Masu zafi
Samu kari