Abba Ya Magantu kan Fitsarar Nuna Dan Kamfai da Mata Suka Yi a Kano

Abba Ya Magantu kan Fitsarar Nuna Dan Kamfai da Mata Suka Yi a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan nuna dan kamfai da wasu mata suka yi a Kano lokacin ziyarar matar shugaban kasa Remi Tinubu
  • Ya bayyana cewa ya kauracewa kafafen sada zumunta saboda abubuwa marasa kyau da ake yi, wanda hakan ne ya sanya bai sam me ya faru ba
  • Duk da haka, Abba Kabir Yusuf ya bayyana mihimmin matakin da ya dauka game da matan da suka nuna dan kamfai a Kano bayan jin labarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana cewa ba shi da hannu a zargin da ke yawo na cewa gwamnatinsa ta raba dan kamfai ga mata a matsayin tallafi.

Duk da yadda labarin ya yadu a kafafen sada zumunta kuma aka jingina masa shi, Abba ya ce an raba dan kamfai din ne ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnatin Abba ce ta ba mata dan kamfai a Kano? An gano gaskiya

Abba Kabir Yusuf da masu nuna dan kamfai
Abba Kabir Yusuf a hagu, matan da suka nuna dan kamfai a dama. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Abba Nasir Bello
Source: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa wasu matasa mata sun fito suna daga jajayen dan kamfai a wani taro da aka shirya domin karrama uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu.

Maganar Abba kan nuna dan kamfai

Da yake jawabi a wani zaman addu’a na musamman da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce bai san da abin da ya faru ba, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa al’ada da addini.

An ga Abba Kabir a wani bidiyo da Premier Radio ya wallafa a Facebook yana gabatar da matan da suka nuna dan kamfai yana barranta daga gare su.

“Kun ji abin da ya faru. Muna nan muna abubuwa aka samu yara ‘yan mata aka ce sun nuna menene menene…
"Gwamna bai san abin da ake ba. Saboda bacin ran irin wadannan abubuwa gwamna ya daina amfani da shafukan sada zumunta, ya gwammace a gaya masa.,”

Kara karanta wannan

Cin bashi: Fadar shugaban kasa ta yi wa Sanusi II martani kan sukar Tinubu

In ji shi.

Ya kara da cewa:

“Amma dole mu yi Allah-wadai da hakan, saboda ba tarbiyyar mu ba ce.

An tara masu nuna dan kamfai

Gwamnan Kano ya bayyana cewa bayan ya samu cikakken bayani, nan take na gayyato ‘yan matan da suka nuna dan kamfai a Kano.

Abba Kabir Yusuf ya ce matan sun yi nadama, sun yi alkawari za su cigaba da aikata ayyuka masu kyau da nuna hali na gari.

Yadda mata suka nuna dan kamfai a Kano
Wasu mata na daga dan kamfai a Kano. Hoto: Abba Nasir Bello
Source: Facebook

An kuma ga matan da suka aikata hakan suna karanta Alkur’ani mai tsarki, suna yin addu’o’i tare da neman gafara kan abin da suka aikata.

An soki nuna dan kamfai a Kano

A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Ibrahim Aliyu Kaduna ya soki yadda mata suka nuna dan kamfai yayin taron siyasa a Kano.

Malamin ya ce nuna dan kamfai abu ne maras kyau kuma, ya sabawa addinin Musulunci da al'adun al'ummar Kano da Arewacin Najeriya.

Haka zalika, wani malamin jami'a dan asalin Kano da ke aiki a kasar Jamus, Dr Muhsin Ibrahim ya soki lamarin, yana kira a hukunta wadanda suka aikata hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng