Ikon Allah: An gano wani yaro Anambra da inyamurai a suka saceshi daga Kano a 2014

Ikon Allah: An gano wani yaro Anambra da inyamurai a suka saceshi daga Kano a 2014

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kano sun tabbatar da ceto wani karamin yaro dan asalin jahar Kano da wasu miyagun mutane yan kabilar Ibo suka sace shi a shekarar 2014 suka kai shi jahar Anambra.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, Abdullahi Haruna ya sanar da sunan wannan yaro da Muhammad Ya’u, inda ya bayyana cewa yaron dan shekara 11 ne.

KU KARANTA: Majalisa za ta amince da kasafin kudin Buhari a watan Nuwamba – Ahmad Lawan

Ikon Allah: An gano wani yaro Anambra da inyamurai a suka saceshi daga Kano a 2014
Muhammad
Asali: Facebook

Kaakaki Haruna ya kara da cewa mutanen da suka sace Muhammad, watau Paul Onwe da matarsa Mercy sun dauke shi ne daga unguwar rukunin gidaje na PRP a cikin karamar hukumar Nassarawa na jahar Kano.

Idan za’a tuna, Paul Onwe da matarsa Mercy suna jiga jigan barayin da suke da hannu wajen satar kananan yara guda 9 daga jahar Kano zuwa jahar Anambra, inda suka sauya musu addini daga Musulunci zuwa Kiristanci, sa’annan suka canza musu sunaye zuwa sunayen Inyamurai.

Kaakakin ya cigaba da cewa rundunonin Yansanda guda biyu na masu yaki da satar mutane da kuma na Puff Adder ne suka ceto wannan yaro a wani samame da suka kai garin Onitsha na jahar Anambra.

Daga karshe Haruna ya yi alkawarin zasu cigaba da bankado duk inda miyagu suke, musamman masu satar kananan yara a jahar Kano domin ceto yaran.

“Rundunar Yansanda tana amfani da wannan dama wajen mika godiyarta ga al’ummar jahar Kano bisa hakuri da suke yi tare da gudunmuwa da suke baiwa rundunar wajen yaki da duk wasu miyagun ayyuka a jahar.” Inji sanarwar.

A wani labarin kuma, jami’an Yansanda dake yaki da yan fashi da makami na rundunar Yansandan Najeriya sun kama tsohon shugaban kamfanin Pijo Najeriya, kuma fitaccen attajiri a garin Kaduna, Alhaji Sani Dauda a kan rikici daya biyo aurar da diyarsa da ya yi.

Surukin ASD, kuma tsohon mijin diyarsa Naseeba ne ya umarci Yansanda su kama Alhaji Sani Dauda, tare da dansa Shehu Dauda da kuma alkalin kotun Musulunci dake Magajin gari, Murtala Nasir, wanda shi ne ya daura auren Naseeba da wani sabon miji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel