Yan majalisa sun tsige mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar Gombe

Yan majalisa sun tsige mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar Gombe

Yayan majalisar dokokin jahar Gombe sun yi awon gaba da mataimakin kaakakin majalisar, Shuaibu Haruna dake wakiltar mazabar Kwami ta gabas ta jahar biyo bayan kada kuri’un rashin gamsuwa da shi da suka yi.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa dan majalisa mai wakiltar Yamaltu Deba ta gabas, Adamu Pata ne ya gabatar da kudurin tsige mataimakin kaakakin, inda nan take dan majalisa mai wakiltar Billiri ta yamma, Tulfugut Kardi ya mara masa baya.

KU KARANTA: Yanzun nan: Gobara ta tashi a fadar gwamnatin jahar Neja dake Minna

Nan take ba tare da bata lokaci ba yayan majalisar suka tabbatar da Alhaju Siddi Buba dake wakiltar Kwame ta gabas a matsayin sabon mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar.

Sai dai kafin darewar Buba wannan kujera mai gwabi, sai da mataimakin masu rinjaye na majalisar, Sadam Bello dake wakiltar mazabar Funakaye ya bayyana bukatar hakan a gaban majalisar, kuma kudurinsa ta samu goyon bayan Mustapha Usman dake wakiltar Gombe ta kudu.

Dan majalisa Pata ya yi duba da sashi na 92 na karkashin sashi na i dana ii na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ne wajen neman tsige Shuaibu Haruna, inda shi kuma kaakakin majalisar, Abubakar Ibrahim ya nada Siddi Buba a matsayin sabon mataimakin kaakakin majalisa kamar yadda sashi na 94 na kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanada.

Kafin bahallatsar tsige mataimakin majalisa tare da nadin sabon mataimakin majalisar, sai da yan majalisar suka tafka muhawara a kan wasu kudurori da gwamnatin jahar Gombe a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Inuwa Yahaya ta tura mata.

Wadannan kudurori biyu sun hada ne da kudurin kafa hukumar asusun kiwon lafiya ta jahar, da kuma hukumar kula da asibitocin gwamnatin jahar, bayan tafka mahawarar sai kaakakin majalisar ya mika kudurorin ga kwamitocin kiwon lafiya da na kudi domin tattara rahoto a kansu.

Daga karshe majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel