Majalisar Amurka Ta Fara Binciken Harin da Trump Ya Kai Arewacin Najeriya a 2025

Majalisar Amurka Ta Fara Binciken Harin da Trump Ya Kai Arewacin Najeriya a 2025

  • Majalisar dokokin Amurka na neman cikakken bayani kan hare-haren sama da dakarun kasar suka kai Najeriya
  • A shekarar 2025 ne Amurka ta kai hari Sakkwato da aka ce da amincewar gwamnatin tarayyar Najeriya
  • ‘Yan majalisa na tambayar hujjar doka, yadda lamarin ya shafi fararen hula da gazawar makaman da aka harba a wancan lokaci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Ƴan Majalisar dokokin Amurka sun bukaci ma’aikatar tsaro ta ƙasar ta Pentagon ta yi cikakken bayani kan hare-haren sama da Amurka ta kai a Najeriya a ranar 25 ga Disamba, 2025, tare da bayyana irin matsayin sojojin Amurka a kasar gaba ɗaya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar cewa sojojin ƙasar sun kai hare-hare kan mayaƙan da ake dangantawa da kungiyar IS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

Majalisar Amurka na binciken hari zuwa Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: @officialABAT, @realDonaldTrump
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa daga baya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an gudanar da wannan aiki a jihar Sakkwato izini da izininta, kuma bai karya ikon Najeriya ko iyakokinta ba.

Yan majalisar Amurka na duba harin Najeriya

Sai dai a wata wasika da aka rubuta ranar 9 ga Maris, 2026 zuwa ga shugaban tsaron Amurka, Pete Hegseth, ‘yan majalisar karkashin jagorancin Sara Jacobs da Jason Crow sun bukaci karin haske kan yadda aka gudanar da aikin.

Wasikar, wacce aka kuma aika wa shugaban rundunar sojojin Amurka a Afirka, Dagvin Anderson, da mikistan harkokin Waje, Marco Rubio, ta nemi bayanai kan batun doka, hadin gwiwa da hukumomin Najeriya, da kuma rahotannin da ke nuna yiwuwar asarar rayukan fararen hula.

‘Yan majalisar sun ambaci cewa gwamnatin Amurka ta bayyana hare-haren a matsayin nasara ba tare da an samu kuskure ba, amma sun ce babu sahihin hujja a bainar jama’a da ke nuna akwai ISIS a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Abin da wasikar majalisar Amurka ta ƙunsa

Wasikar ta kuma nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu makamai sun kasa aiki yadda ya kamata. An ce akalla makamai masu linzami guda hudu cikin 16 sun gaza kai hari yadda aka tsara, inda wasu suka fada kan gonaki da gidajen jama’a.

Haka kuma, an ce an gano wasu makamai da ba su fashe ba a wuraren fararen hula, ba tare da alaka da mayaƙa ban da ke tayar da ƙayar baya ba.

'Yan majalisar sun bayyana cewa akwai rahotannin tura kusan sojoji 200 na Amurka zuwa Najeriya domin horas da jami’an tsaro, tare da ci gaba da taimakon bayanan sirri da dabarun kai hari.

Amurka ta kawo hari Najeriya a 2025
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Donald Trump a dama Hoto: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Facebook

Sun gabatar da tambayoyi 11 ga ma’aikatar tsaro, daga ciki har da adadin hare-haren da aka kai tun daga Disamba 2025, wadanda aka kai wa hari, da kuma wadanda suka mutu ko suka jikkata.

Har ila yau, sun nemi a bayyana irin hadin gwiwar da aka yi da gwamnatin Najeriya kafin, yayin da kuma bayan kai hare-haren, ciki har da raba bayanan sirri da yadda aka sanar da jama’a.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya

Babban abin da ya dauki hankali shi ne tambayar da suka yi kan hujjar doka da ta bai wa Amurka damar kai irin wadannan hare-hare, tare da tambayar dalilin da ya sa ba a sanar da Majalisa ba kamar yadda dokar yaki ta 1973 ta tanada.

Sun bukaci a yi bayani kan kudin da aka kashe wajen kai hare-haren, daga ciki har da makamai, jami’ai, sa ido da kuma tantance sakamakon hare-haren.

Amurka ta kawo hari Najeriya

A baya, mun wallafa cewa kasar Amurka ta ce ta kai hare-hare kan yan ta'adda da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ne bisa bukatar gwamnatin kasar.

Harin ya auku a Arewa maso Yammacin kasar, a yankin jihar Sakkwato inda jama'a suka ji ƙarar da ta girgiza wasu gidaje tare da daga hankulan mazauna yankunan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kai harin ne bayan gargaɗin cewa hakan za ta faru idan ba a daina kashe kiristoci ba, wanda ya ace ana yi da gangan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng