Musulunci ya samu karuwa: Gari guda sukutum sun Musulunta baki dayan su

Musulunci ya samu karuwa: Gari guda sukutum sun Musulunta baki dayan su

- Allah mai girma da buwaya ya shiryar da wani kauyen kiristoci inda dukkansu suka koma musulunci

- Wani kauye da ke kasar Philippine mai kunshe da kiristoci 250 ya koma kauyen musulmai bayan da suka saurari wa'azin wata kungiyar musulunci

- Kungiyar da asalinta a kasar Birtaniya take ta bayyana cewa mutanen sun shiryu ne saboda kalmar Allah da suka je suka yada a garin

Allah mai girma da jin kan bayinsa, shi ke shiryarwa da kuma batarwa. Wata mu'ujiza ta faru a wani karamin kauyen kiristoci mai dauke da mutane dari biyu da hamsin a yankin tsakiyar kasar Philippine.

Wata kungiyar Musulmai ta kasar Birtaniya wacce ta shahara a bincike da koyar da ilimin addinin Islama ne suka ga wannan ikon Allah, yayin da kauyen gaba daya suka karbi addinin Musulunci.

Kungiyar ta amsa gayyatar wani tubabbe ne da yayi shekaru 20 yana aikin ganin ya yada addinin Musulunci a cikin rayuwar Filipinos din. Kungiyar ta isa ne inda ta samu Abu Bakr, wanda ya Musulunta a tsibirin Bayatan dake a yankin Cebu na kasar Philippines din.

KU KARANTA: An yiwa yara 99 da suka shafe kwanaki 40 ba su rasa sallah a jam'i ba kyautar kekuna

Kafin su je kauyen, su kwashi abinci don rabawa 'yan kauyen a matsayin kyauta garesu.

Bayan kungiyar sun isa kauyen, sai suka hada taro don mika sakon Musulunci ga Kiristocin, Kiristocin kusan su dari biyu da hamsin wa'azin Abu Bakr da sauran 'yan kungiyar ya ratsa su .

Sun yi bayani akan kamanceceniya tsakanin musulunci da Kiristanci tare da sakon gaskiya na annabi Isah wanda suka dukufa bauta wa, a take Kiristocin suka karbi addinin Musulunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng