An kama matashi mai yaudarar mata da soyayya sai an zo daurin aure ya bace da dukiyoyinsu

An kama matashi mai yaudarar mata da soyayya sai an zo daurin aure ya bace da dukiyoyinsu

Hukumar 'yan sanda ta cafke wani mutum mai suna Uchenna Duru akan zarginsa da ake da damfarar wata mata inda ya tsere a ranar aurensu.

Kamar yadda rahoto daga Daily Post ya bayyana, an kama Uchenna ne bayan da wata mata mai suna Ruth Abdullahi ta kai wa ‘yan sanda rahoton yadda ya damfareta wasu kudade da mota kirar Toyota Camry mai lamba GU 514 LV.

An zargi cewa, Uchenna yayi alkawarin auren wata kawar Ruth mai suna Adams Dora wacce ya hadu da ita a kafar sada zumuntar zamani.

DUBA WANNAN: Oshiomhole: Tsohon dan takarar gwamna a PDP ya koma APC a jihar Edo

An gano cewa, bayan an cafke wanda ake zargin, wata mata mai suna Faith Eriamiatoe ta bayyana gaban hukumar inda take bayyana musu cewa ya damfareta naira dubu saba’in da uku tare da alkawarin zai aureta. Ya kara da bayyana mata cewa, zai kawo mata kayan da hukumar kwastam suka yi gwanjonsu.

Bayan da jami’an ‘yan sandan suka cafke Uchenna, yace bai damfari matar ba. Ya tsere ne bayan da ya gano tana da ‘ya’ya hudu.

Na karanci fannin shari’a ne a jami’ar jihar Imo amma banje makarantar horar da lauyoyi ba. Ina aikin wuta ne kuma ina shigo da kayayyakin ne daga kasashen ketare. Ban damfari matan ba. Duk abinda suke fada karya ne. Na biya sadakin Dora, tserewa nayi bayan da na gano tana da ‘ya’ya hudu kuma bazan iya kula dasu ba,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel