Iran Ta Kafa Tarihi a Duniya bayan Shiga Kwana na 57 a Yakinta da Isra’ila
- Kasar Iran ta shiga tarihin duniya bayan katse intanet na kwanaki 57 ba tare da tsayawa ba yayin da ake ci gaba da yaki
- Katsewar ta fara ne bayan hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila a Tehran, lamarin da ya keɓe ‘yan ƙasar daga duniya
- Duk da matsin lamba da rikicin diflomasiyya da Amurka, Iran ta ƙi shiga tattaunawa kai tsaye, yayin da ake ci gaba da takaddama
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ƙasar Iran ta fuskanci katsewar intanet na tsawon kwanaki 57 ba tare da tsayawa ba a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya zama mafi tsawo a tarihin duniya a matakin ƙasa da aka taba yi.

Source: Getty Images
Rahotanni daga Al Jazeera sun nuna cewa an fara katsewar ne bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai a Tehran a ranar 28 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Yadda yakin Iran da Isra'ila ya barke
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila wacce ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.
Yakin akalla ya kwashe mako uku kenan tun bayan harin farko a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an tsaro.

Source: Getty Images
Yadda katse intanet ya shafi mutanen Iran
Majiyoyi suka ce katsewar ta hana muryoyin ‘yan ƙasar bayyana, ta raba iyalai da abokai, tare da jawo mummunar illa ga tattalin arziki.
Haka kuma, wannan mataki ya ware ‘yan Iran daga sauran duniya a lokacin da yankin ke cikin tashin hankali mai tsanani.
A wani ɓangare, rikicin diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka ya ƙara tsananta, inda Iran ta dage cewa ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye ba.
Takaddama kan batutuwan nukiliya, bude mashigar Hormuz, da ayyukan soji na Isra’ila a Lebanon na ci gaba da hana cimma matsaya, cewar The Arabian Stories.
Yayin da Amurka ke ƙara ƙarfafa rundunarta da sanya takunkumi, Iran ma ta ɗauki matakan ramuwar gayya da suka shafi harkokin sufuri da kasuwanci.
Har yanzu dai ana cikin rashin tabbas kan ko za a ci gaba da tattaunawa, yayin da matsin lamba ke ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Iran ta yankewa dan leken asiri hukuncin kisa
Mun ba ku labari a baya cewa hukumomin Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ke yada bayanan sirrinta ga kasar Isra'ila da suke rikici.
An kama mutumin mai suna Mehdi Farid da laifin yi wa Isra’ila leƙen asiri tare da tura bayanan sirri ga Mossad yayin da ake ci gaba da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce marigayin ya yi aiki a wani bangare mai matuƙar muhimmanci na tsaron farar hula, inda ya yi amfani da damar da yake da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
