Cole Allen: Abubuwan Mamaki game da Matashin da Ya Kai Hari kan Su Donald Trump
- Jami’an tsaron Amurka sun bayyana Cole Tomas Allen, mai shekaru 31, a matsayin mutumin da ake zargi da buɗe wuta a fadar White House
- Allen, wanda kwararre ne a fannin injiniya da kimiyyar kwamfuta, kai harin da bindiga kirar shotgun a taron da Donald Trump ya halarta
- Masu bincike na nazarin na'urorinsa na lantarki domin gano dalilin kai wannan hari da ya girgiza manyan kusoshin gwamnatin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – Jami’an tsaro sun bayyana ainihin asalin mutumin da ya kai harin bindiga kan su Donald Trump a wurin taron cin abincin dare na kungiyar 'yan jaridun fadar White House a daren ranar Asabar.
Cole Tomas Allen, mai shekaru 31, mazaunin garin Torrance ne da ke jihar California, kuma binciken farko ya nuna cewa mutumin kwararre ne a fannin kimiyya da fasaha wanda babu wanda ya taba tsammanin zai aikata hakan.

Source: Getty Images
Abubuwan sani game da Cole Tomas Allen
A cewar shugaban ’yan sandan yankin Columbia, masu bincike sun yi amannar cewa Allen ya sauka ne a matsayin bako a otal din Washington Hilton inda ake gudanar da taron, in ji rahoton Reuters.
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun bayyana cewa maharin yana dauke da bindiga kirar shotgun, inda ya bude wuta ga wani jami’in tsaor a wajen dakin taron da Shugaba Donald Trump da iyalinsa suke.
Bincike a shafukan sada zumunta da kuma bayanan LinkedIn sun nuna cewa Cole Allen hazikin injiniya ne kuma masanin kimiyyar kwamfuta.
Ya kammala digirinsa na farko a fannin injiniyan kanikanci daga fitacciyar jami'ar Caltech a shekarar 2017, sannan ya samu digiri na biyu a fannin kimiyyar kwamfuta daga jami'ar California State a shekarar 2025.
Wata sanarwa daga jami'ar Caltech ta tabbatar da cewa tabbas ya kammala karatu a wurin a shekarar 2017, kuma ya taba zama mataimakin malami a jami'ar.
Matashi ya yi ba-zata a kai hari White House
Dangane da kwarewarsa, Allen ya bayyana kansa a matsayin injiniyan kanikanci da masanin kwamfuta ta hanyar karatu, mai samar da wasannin bidiyo ta hanyar gogewa, kuma malami.
Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa ya taba samun kyautar "Malamin Watan Disamba" a shekarar 2024 a wata cibiyar koyarwa mai suna C2 Education.
Wannan yanayi na nuna cewa maharin ba mutumin da aka sani da aikata miyagun laifuka ba ne, sai dai wanda ya mayar da hankali kan fannin kimiyya da fasaha kadai a shafukansa na intanet.

Source: Facebook
Bincike kan dalilin kai harin
Duk da cewa jami'an tsaro sun cafke shi, har yanzu ba a tantance dalilin da ya sa ya kai harin ba, in ji rahoton NBC News.
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun tabbatar da cewa ya bude wuta ne a daidai lokacin da manyan kusoshin gwamnatin Amurka, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance da wasu ministoci, ke halartar taron.

Kara karanta wannan
Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House
Hukumomin tsaro na ci gaba da nazarin bayanan da suka samu daga dakin da ya kama a otal din da kuma na'urorinsa na lantarki.
Jeanine Pirro, lauyar gwamnati, ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a ranar Litinin a gaban kotun tarayya.
Martanin Trump kan harin Allen
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya tsallake rijiya da baya bayan wani harbin bindiga da ya afku a yayin da take wani taro a fadar White House.
Maharin, mai suna Cole Tomas Allen, ya bude wuta ne a wajen dakin taron, inda jami'an tsaro suka yi gaggawar fitar da Trump da maidakinsa.
Duk da wannan hari, Trump ya jaddada cewa babu abin da zai dakatar da shi daga yaki da kasar Iran, wanda a halin yanzu yake fuskantar kalubale.
Asali: Legit.ng

